Matar Aure Ta Yanke Al'aurar Mijinta Yana Kwance, Ta Dafa Abinci da Shi

Matar Aure Ta Yanke Al'aurar Mijinta Yana Kwance, Ta Dafa Abinci da Shi

  • Rundunar ‘yan sanda ta kama wata mata a Brazil bisa zargin yanke al'aurar mijinta, ta dafa a cikin miya bayan ta hallaka shi saboda kishi
  • An gano gawar mamacin ba tare da gabansa ba a kusa da gidansu bayan danginsa sun bayyana damuwa kan halin da aka same shi a ciki
  • Rahotannin da aka samu daga baya sun ce matar ta amsa aikata kisan da kuma yin amfani da sassan jikin mijinta a cikin abincin da ta dafa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Brazil - Wani mummunan lamari ya afku a garin Acrelandia da ke yammacin Brazil, wata mata ke fuskantar tuhumar kisan mijinta da yanke gabansa, sannan ta dafa a cikin miya.

Matar wadda ba a bayyana sunanta ba ta yi kisan ne domin huce haushi bayan ta kama mijin nata yana kallon finafinan batsa a gidansu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa fadar mai martaba, sun bulale fadawa sun tafi da Sarki

Brazil
Mata ta yanke gaban mijinta a Brazil. Hoto: Daily Mail
Source: UGC

Rahoton Daily Mail ya bayyana cewa an gano gawar mamacin, mai shekaru 37, a kusa da gidansu bayan danginsa sun nemi shi ba su same shi ba.

Mata ta dafa abinci da al'aurar mijinta

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa matar ta hallaka mijinta, sannan ta yanke gabansa da kuma wasu sassa na jikinsa, ta hada da su a cikin miyar wake da ta dafa.

Bayan kama ta, Tribune ta wallafa cewa ta amsa laifinta ga ‘yan sanda, tana mai bayyana cewa ta aikata hakan ne saboda fushi da kishi.

Ba a tabbatar ba ko ita kadai ce ta ci miya ko kuma akwai wasu da suka ci abincin ba tare da sanin abin da ke ciki ba.

An yanke al'aurar wani mutum a Peruibe

Lamarin na zuwa ne watanni bayan wani dattijo dan shekaru 60, Celso Marques Ferreira, ya mutu a birnin Peruibe, inda aka tsinci gawarsa ba tare da gabansa da wani bangare na zuciyarsa ba.

Kara karanta wannan

'Da yamma suka tare mu,' Yan daba sun dawo kwace ido na ganin ido a Kano

Wata mata mai suna Josefa Lima de Sousa, wadda aka fi sani da “Gringa”, ta amsa cewa ita ce ta aikata kisan bayan ta gano cewa mamacin mai fyade ne.

Josefa Lima de Sousa ta bayyana cewa ta dafa zuciyarsa da gabansa sannan ta ci bayan ta kashe shi.

Mata yanke al'aurar mijinta a Philippines

Haka zalika, a bara wata mata a birnin Baguio na Philippines ta yanke al’aurar mijinta yayin da suke jima’i bayan ya ambaci sunan wata mace.

Jami’an ‘yan sanda sun kama matar kuma suka kwato wuka da sassan al’aurar da ta yanke. Likitoci sun yi kokarin mayar da sassan amma hakan bai yi nasara ba.

Jami’ai sun ce matar tana fuskantar tuhumar illa wa al'aura saboda kishi kuma za a gurfanar da ita.

Kotun
Za a gurfanar da matar da ta yanke gaban wani mutum a kotu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An yanke al'aurar saurayi a jihar Rivers

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun kama wata mata da ake zargi da yanke al'aurar wani mutum a Rivers.

Ana zargin cewa matar ta yanke al'aurar mutumin ne sakamakon wani sabani da suka samu a tsakaninsu.

Rundunar 'yan sandan jihar Rivers na cigaba da bincike a kan lamarin tare da tattabar da cewa za a gurfanar da matar idan an kammala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng