Babbar magana: Wani miji ya like al'aurar matarsa da 'super glue' don kar ta ci amanarsa

Babbar magana: Wani miji ya like al'aurar matarsa da 'super glue' don kar ta ci amanarsa

Wani magidanci ya yanke shawarar like gaban matarsa bayan da ya gano tana bin maza a duk lokacin da ya bar garin don harkar kasuwancinsa.

Dennis Mumo, babban mutum ne da ake ganin kimarsa a Kitui. Son da yake wa matarsa ne da rashin son rabuwa da ita ne yasa ya like gabanta da sufa gulu har zuwa ranar da zai dawo daga balaguron kasuwancinsa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, a ranar Juma'a ne aka kama Dennis da laifin wannan aikin da yayi a kan matarsa.

An mika matar asibiti inda aka dinga aiki don shawo kan wannan matsalar.

Babbar magana: Wani miji ya like al'aurar matarsa da 'super glue' don kar ta ci amanarsa
Babbar magana: Wani miji ya like al'aurar matarsa da 'super glue' don kar ta ci amanarsa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kuma dai: Yawan alkalan kotun koli ya sake ragu wa zuwa 13

A lokacin da yake amsa tuhumarsa da 'yan sanda suke yi, ya amsa laifinsa tare da karbar duk hukuncinsa amma ya ce dole ce ta sa yayi hakan don tseratar da aurensu.

Ya ce, ya samu labari ne a kan yadda matarsa ke bin maza suna lalata idan baya gari. Don haka ba zai iya hakuri ba idan ta kwaso musu cuta.

Yana da hotunan tsiraicin matarsa da wasu mazan tare da sakonnin kar ta kwana da suke musaya da masoyanta na waje.

Za a gurfanar da mijin a yau Litinin a kan cin zarafin matar sa da yayi. Ita ma matar za ta gurfana a gaban kotu a kan laifin bin mazan waje bayan tana da aure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel