Wata lauya ta kashe mijin ta sannan ta datse masa al’aura

Wata lauya ta kashe mijin ta sannan ta datse masa al’aura

A yau, Litinin, ne wata babbar kotun jihar Legas dake zaman ta a Igboser ta bayar da umarnin a tsare wata lauya, Udeme Otike-Odibi; mai shekaru 48 saboda kisan mijin ta, Symphorosa Otike-Odibi, mai shekaru 52.

An zarge tad a yanke al’aurar mijin nata bayan ta kashe shi.

Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da Udeme bisa tuhuma guda biyu da suka hada da; kisan kai da wulakanta gawa. Ta musanta tuhumar da ake yi mata.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sunmonu Babatunde, ya shaidawa kotu cewar, wacce ake zargin ta aikata laifin ne ranar 3 ga watan Mayu a gidan su dake rukunin gidajen Diamond Estate dake unguwar Sangotedo a Lekki ta jihar Legas.

Wata lauya ta kashe mijin ta sannan ta datse masa al’aura

Udeme da mijin ta da ta kashe

Ya shaidawa kotun cewar ta caccakawa mijin nata wuka sannan ta yanke masa al’aura bayan ya mutu.

Alkalin kotun, Adedayo Akintoye, ya bayar da umarnin a tsare Udeme a gidan yari sannan ya daga sauraron karar zuwa ranakun 8 da 9 ga watan Oktoba.

DUBA WANNAN: Karshen lalacewa: Wani uba ya yiwa diyar sa mai shekara 1 kacal fyade

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar, ko a baya saida wata kotun majistare ta bayar da umarnin tsare Udeme a gidan yari kafin darektan hukumar shigar da kararraki gaban kotu na jihar Legas ya kamala nazarin takardun tuhumar da ake yi mata domin bayar da shawara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel