'Yar Najeriya na Fuskantar Barazana a Amurka, Za Ta Iya Shafe Shekaru 10 a Kurkuku
- Funke Iyanda, wata mazauniyar Amurka, na fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bisa zargin karɓar tallafi ba bisa ka’ida ba
- Rahotanni sun bayyana cewa Iyanda ta samu $40,980 daga ma’aikatar ƙwadago ta Pennsylvania ta hanyar amfani da bayanan wani mutumi
- Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta ce idan aka tabbatar da laifin Iyanda, za ta biya tarar $250,000 ko daurin shekaru 10 ko kuma duka biyun
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Wata ƴar mazauniyar Amurka, Funke Iyanda, na fuskantar barazanar shafe tsawon shekaru 10 a gidan yarin ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa, Funke Iyanda, na fuskantar ɗauri ne bayan an tuhume ta da zambar $40,980 daga tallafin rashin aikin yi.

Source: Getty Images
'Yar Najeriya na fuskantar dauri a Amurka
A cewar ma’aikatar shari’a ta Amurka, Iyanda na zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, kuma ba ta da ikon karɓar wannan tallafin da ta nema, inji rahoton Punch.
Rahoton ya bayyana cewa daga Mayun 2020 zuwa Mayun 2021, Funke Iyanda ta yi amfani da bayanan wani mutum don karɓar tallafin kudi.
Wani sashe na rahoton ya ce:
“Wata ‘yar Nijeriya da ke zaune a garin Pittsburgh, jihar Pennsylvania, na fuskantar tuhuma kan laifin wawure dukiyar gwamnati.”
An bayyana Iyanda, mai shekaru 43, a matsayin wadda ake tuhuma a cikin ƙarar da gwamnatin Amurka ta gabatar gaban kotu, kan tuhuma ɗaya tal.
Yadda 'yar Najeriya ta yi zamba a Amurka
Rahoton ya nuna cewa a tsakanin Mayun 27, 2020, zuwa Mayun 24, 2021, Iyanda ta karɓi kuɗi har $40,980 daga ma’aikatar ƙwadago ta Pennsylvania, duk da cewa ba ta da hurumin karɓar wannan tallafi.
Idan aka tabbatar da laifinta, Funke Iyanda na iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 a kurkuku tare da tarar $250,000.
“Doka ta tanadi hukuncin dauri na shekaru 10 da tarar $250,000, ko duka biyun,” in ji rahoton.
An bayyana cewa hukuncin da za a yanke zai dogara ne da yadda laifin ya yi tsanani da tarihin aikata laifuffuka na wadda ake tuhuma.
An daure farfesa shekara 2 a kurkuku

Source: Getty Images
Sanarwar ma'aikatar shari'ar ta jaddada cewa tuhuma ba ya nufin laifi, har sai kotu ta tabbatar da hakan bisa hujjojin da aka gabatar mata.
A baya, an yanke wa wani Farfesa ɗan asalin Najeriya, Gordian Ndubizu, hukuncin shekaru biyu a kurkuku kan kin biyan haraji a Amurka.
Farfesa Ndubizu da matarsa sun samu kuɗin shiga na $3.28m, amma sun guji biyan haraji na $1.25m daga shekarar 2014 zuwa 2017.
Amurka ta cafke dan Najeriya kan zambar $10m
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Amurka ta cafke wani ɗan Najeriya, Yomi Olayeye, bisa zargin karkatar da $10m daga tallafin COVID-19 da ake ba marasa aikin yi a ƙasar.
Ana tuhumar Olayeye da laifuffuka da suka haɗa da haɗa baki, satar kuɗi ta intanet, da satar bayanai, inda aka kama shi a filin jirgin sama na John F. Kennedy.
A cewar ma’aikatar shari’a ta Amurka, idan aka same shi da laifi, Yomi Olayeye zai fuskanci hukuncin daurin shekaru 20 a kurkuku tare da tarar $250,000.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

