An yankewa mai sana’ar sayar da tabar wiwi shekaru 2 a kurkuku

An yankewa mai sana’ar sayar da tabar wiwi shekaru 2 a kurkuku

- Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan daka

- Wani matashi ya girbi abin da ya shuka a gaban kotu sakamakon kama shi da laifin safarar wiwi

- Sai dai bayan yanke masa hukuncin yayi jawabi mai sosa rai dake nuna nadama

Wata babbar kotu a jihar Legas ta yankewa wani mai suna Yusuf Abdulkareem hukuncin shekaru biyu a kurkuku bisa kama shi da laifin safarar tabar ganyan wiwi mai nauyin 1kg.

An yankewa mai sana’ar sayar da tabar wiwi shekaru 2 a kurkuku
An yankewa mai sana’ar sayar da tabar wiwi shekaru 2 a kurkuku

Hukuma yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NAFDAC) ce ta gurfanar da wanda ake zargin gaban mai shari’a Chuka Obiozor bisa kama shi da laifin safarar wiwin.

Kuma ya amsa laifinsa ba tare da wani ja’in ja ba.

KU KARANTA: Karshen aikin sojojin Najeriya 320 yazo amma ckin salama har da tagomashi

Mai gabatar da kara Mr Jeremiah Aernan ya gabatarwa da kotun wasu shaidu domin tabbatar da laifin wanda ake karar, daga cikin shaidun akwai; takardara sakamakon binciken likita na sanfurin jakar tabar wiwin da kuma tulinta da suka kama shi da ita, tare da jawabinsa da aka dauka.

A don haka ne mai shari’a Obiozor ya tabbatar da samun wanda ake zargin da laifi, sannan ya yanke masa hukunci farawa tun daga ranar da aka fara kama shi tun ranar 10 ga watan Afrilu.

Dokar NDLEA dai ta tarayya sashi na 11(c) Cap. N30 2004, da ta zayyana duk wani ta’ammali da tabar wiwi laifi ne babba kamar yadda yake ga sauran kayan maye irinsu hodar iblis da muggan kwayoyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng