Mummunan Hatsarin Mota Ya Rutsa da Fitacciyar Mawakiya, Ta Rasu Tana da Shekaru 63

Mummunan Hatsarin Mota Ya Rutsa da Fitacciyar Mawakiya, Ta Rasu Tana da Shekaru 63

  • Fitacciyar mawakiya kuma jarumar fina-finai, Angie Stone, ta rasu tana da shekaru 63 bayan hatsarin mota ya rutsa da ita a yankin Alabama
  • Hatsarin ya faru ne yayin da ita da tawagarta ke kan hanyarsu ta zuwa Atlanta bayan sun kammala gabatar da wasa a Mobile, Alabama
  • Angie Stone ta fara shahara tun a shekarun 1970 a matsayin ‘yar kungiyar mawaka ta 'The Sequence', wacce ta yi fice a wakokin hip-hop
  • An rahoto cewa mawakiya Angie Stone na shirye-shiryen gabatar da wani gagarumin abu da zai rikita Birtaniya kafin mutuwa ta riske ta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Fitacciyar mawakiya kuma jarumar fina-finai, Angie Stone, ta rasu tana da shekaru 63 bayan hatsarin mota a Montgomery, Alabama.

Hatsarin ya faru ne ranar Asabar yayin da ita da tawagarta ke kan hanyar zuwa Atlanta bayan wani wasa da suka gabatar a Mobile, Alabama.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta fitar da sanarwa kan ganin watan Ramadan na 2025

An sanar da mutuwar fitacciyar mawakiyar R&B, Angie Stone, tana da shekaru 63
Fitacciyar mawakiya, Angie Stone, ta rasu sakamakon hatsarin mota a Amurka. Hoto: @angiestone
Asali: Twitter

Mawakiya Angie Stone ta shara tun a 1970

Rahotanni daga jaridar TMZ sun bayyana cewa motarsu ta yi karo da wata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Angie Stone.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Angela Laverne Brown, wanda shi ne sunan yankan Angie Stone, ta fara shahara tun a shekarun 1970 a matsayin 'yar tawagar mawakan The Sequence.

The Sequence na daga cikin kungiyoyin mata na farko da ke wakokin hip-hop, kuma sun samu daukaka da wakarsu mai suna 'Funk You Up'.

Wakar ta yi tasiri har aka yi amfani da ita a cikin wakar 'Uptown Funk' ta Bruno Mars da 'Keep Their Heads Ringin’ na Dr. Dre.

Komawar Angie wakokin R&B da shahararta

Rahoton shafin WikiPedia ya nuna cewa, daga baya Angie Stone ta koma nau'in wakar R&B, inda ta shiga tawagar Vertical Hold a shekarun 1990.

Ta samu nasara sosai da wakarta 'Seems You’re Much Too Busy', wacce ta ja hankalin masoyan wakokin R&B.

Kara karanta wannan

Tsohon makusancin Peter Obi ya hango rugujewar LP, ya fadi makomarsa a 2027

A 1999, Angie Stone ta saki kundinta na farko mai suna 'Black Diamond*, wanda ya samu karbuwa matuka a duniya.

Wakar 'No More Rain (In This Cloud)' daga wannan kundin ta tabbatar da matsayinta a fagen rera wakoki masu ratsa zuciya, a cewar rahoton Punch.

Mutuwar mawakiya Angie ta girgiza mutane

Fitacciyar mawakiyar duniya, Angie Stone ta mutu a hatsarin mota
Mutane sun fara tuturwar mika sakon ta'aziyya na mutuwar mawakiya Angie Stone. Hoto: @angiestone
Asali: Twitter

Mahogany Soul (2001) na daga cikin fitattun kundinta, inda ta fitar da wakar 'Wish I Didn’t Miss You', wacce ta shahara sosai a duniya.

Baya ga waka, Angie Stone ta taka rawa a fina-finai irinsu 'The Hot Chicck' da kuma fim din 'The Fighting Temptations'.

Stone ta mutu ta bar yara biyu; Diamond, daga auren ta da Rodney Stone, da kuma Michael, daga alakar soyayyarta da D’Angelo.

Mutuwarta ta girgiza masana’antar waka da fim, inda mutane da dama ke tururwar mika ta’aziyyarsu tare da yabon rawar da ta taka.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

An rahoto cewa makiya Angie Stone na tsakiyar shirye-shiryen kawo wata gagarumar tafiya a Birtaniya a lokacin da mutuwa ta cimmata.

Shahararriyar mawakiyar yabon addini ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mawakiyar yabo a Najeriya, Aduke Ajayi, wacce aka fi sani da Aduke Gold, ta rasu bayan ta yi fama da rashin lafiya.

Aduke Gold ta shahara a fagen wakokin yabo, inda mutuwarta ta jefa al’ummar Kiristoci cikin alhini da kaduwa, yayin da ake ta tururuwar mikawa iyalanta sakon ta'aziyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.