Fitacciyar Mawakiyar Yabon Addini Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Fitacciyar Mawakiyar Yabon Addini Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Matashiyar mawakiyar yabo na addinin Kirista a Najeriya, Aduke Ajayi ta yi bankwana da duniya a jiya Litinin
  • Mariyayiyar da aka fi sani da Aduke Gold ta yi shura a fagen wakokin yabo inda al'ummar Kiristoci suka kadu
  • Mutane da dama sun kadu da samun labarin mutuwar Gold wacce ta yi shura tare da nishadantar da jama'a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - An shiga jimami bayan sanar da rasuwar fitacciyar mawakiyar yabo na addinin Kirista bayan fama da jinya.

An samu labarin rasuwar marigayiya Aduke Ajayi da aka fi sani da Aduke Gold ne a jiya Litinin 12 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Direban adaidaita sahu ya maida jakar kudin da ya tsinta, yan sanda sun sa cigiya

Mawakiyar yabo a Najeriya ta kwanta dama
Fitacciyar mawakiyar yabo, Aduke Gold ta riga mu gidan gaskiya. Hoto: @adukegold1.
Asali: Instagram

Mawakiyar addini ta yi bankwana da duniya

An fara samun labarin rasuwar marigayiyar bayan GoldMynetv ta tabbatar da haka a shafin Instagram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har il yau, mawakiya Esther Igbekele ta tabbatar da mutuwar Gold a cikin wata sanarwa a kafar sadarwa.

Esther ta ce duk da gagarumar gasa da ke cikin masana'antar wakokin yabo amma Gold ta ba da muhimmiyar gudunmawa saboda jajircewarta.

Ta ce kwarewarta a harkar wakokin da muradin hakan sun samar da mata yawan masoya wanda ko bayan ba ta nan za ta cigaba da kafa tarihi.

Yaushe mawakiyar ta riga mu gidan gaskiya?

Wata majiya ta tabbatar da cewa Gold ta rasu ne a jiya Litinin a asibitin koyarwa da ke Ibadan a jihar Oyo.

Majiyar ta ce Gold ta rasu ne bayan shafe akalla watanni biyu ba tare da isasshen lafiya ba.

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan PDP zai sauya jam'iyya, tsageru sun jefa 'bam' ofishin APP

Mutuwar mawakiyar ya tayarwa jama'a hankali musamman al'ummar Kiristoci inda suka shiga jimami.

Mawakiyar addinin Kirista ta rasu

A wani labarin, mun kawo muku cewa fitacciyar mawakiyar addinin Kirista, Morenikeji Adeleke ta riga mu gidan gaskiya.

Marigayiyar da aka fi sani da Egbin Orun ta rasu ne a ranar Asabar 28 ga watan Afrilun 2024 sai dai ba a bayyana dalilin mutuwar tata ba.

Mawakiya Esther Igbekele ta nuna alhini kan rasuwar marigayiyar inda ta ce mace ce mai sauƙin kai wacce ta taimake ta a rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.