Wata sabuwa: Za a kama fitattun mawakan masana'antar Kannywood guda biyar
- Bayan kama fitaccen daraktan shirya fina-finan Hausa na Kannywood, alamu sun nuna cewa kungiyar tace fina-finan Hausa ba ta tsaya a nan ba
- Inda ta bayyana cewa akwai yiwuwar za ta kama wasu fitattun mawakan Kannywood guda biyar
- Wannan rahoton dai gidan rediyon Freedom ne ya bayyana haka, inda kuma aka kira mawakan aka ji ta bakinsu
Bayan kama shahararren Daraktan shirya fina-finan Hausa Sunusi Oscar 442 da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta yi, gidan rediyon freedom mai zaman kansa na jihar Kano ya bayar da rahoton kama wasu fitattun mawakan Kannywood guda biyar da ake tunanin kungiyar za ta kara yi.
Mawakan wadanda suka nuna goyon bayansu ga siyasar tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso sun hada da:
1. Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan Waka.
2. Naziru Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka, wwanda kuma Sarkin Kano ya bai wa Sarautar Sarkin Wakar Kano.
3. Musbahu Ahmad
4. Ali Artwork wanda aka fi sani da Madagwal
5. Mustapha Badamasi Naburuska
KU KARANTA: Gaba da gabanta: Mata Musulmai guda biyu da suka tsonewa Trump da kasar Isra'ila ido a duniya
A lokacin da manema labarai suka tuntubi gidan rediyon freedom din sun tabbatar da cewa sun ji ta bakin mawakan kuma sun tabbatar da wannan batu sai dai kawai Aminu ALa ne aka samu wayarsa a kashe.
Sai dai shi kuma shugaban hukumar tace fina-finai da aka tuntubeshi, Aminu Afakallahu domin aji ta bakinsa ya karyata wannan magana inda ya ce:
"Wannan batu ba gaskiya ba ne, sai dai idan dama suna aikata laifin ne wanda yasa yanzu suke neman mafaka ko da ace za a kama su. Kuma hakan ba zai hana mu kama duk wanda muka samu da laifi ba," in ji shugaban hukumar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng