'Yan Tawaye Sun Karbe Syria, An Nemi Shugaban Kasa Bashar Al Assad An Rasa a Damascus
- Ana fargabar yan tawaye sun kwace iko a kasar Syria yayin da ake tunanin shugaban kasar ya tsere
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Bashar al-Assad ya tsere daga birnin Damascus yayin da yan tawayen suka kwace iko
- Wannan ya biyo bayan shafe shekaru 13 ana yakin basasa a kasar Syria karkashin mulkin Bashar Al-Assad
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Damascus, Syria - Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad ya tsere daga babban birnin kasar, Damascus.
Hakan ya biyo bayan shigowar dakarun ‘yan tawaye wanda ake tabbatar sun kwace iko a kasar da kuma gwamnati.
Yan tawaye sun kifar da gwamnatin Al-Assad
Rahoton BBC News ya ce lamarin na iya kawo karshen yakin basasar kasar da ya shafe shekaru 13 ana yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Asabar 7 ga watan Disambar 2024 ‘yan tawaye suka ayyana nasarar kwace iko inda suke murna a birnin.
Haka zalika, an ruwaito cewa dubban fursunonin siyasa sun kubuta daga gidajen yari na gwamnati, abin da ke nuna ƙarshen mulkin Assad.
Fiye da shekaru goma, an zargi gwamnatin Assad da take hakkin dan Adam ciki har da zarge-zargen kisan kiyashi da amfani da makaman gas akan fararen hula.
An soki gwamnatin Assad kan zubar da jini
Gwamnatinsa ta sha suka kan matakin da ta dauka game da zanga-zanga tun lokacin juyin-juya-haki na kasashen Larabawa a shekarar 2011, cewar rahoton Reuters.
Duk da cewa ba a tabbatar da inda Assad yake ba, shugabannin ‘yan tawaye sun bayyana tafiyarsa da cewa “karshen zalunci” a kasar Syria.
“Wannan wata babbar nasara ce ga mutanen Syria da suka sha wahala da ba za a iya misalta ba,”
- Cewar kakakin ‘yan tawaye
Mutum 44,000 sun mutu a Syria sa Turkiyya
Kun ji cewa Gagarumar girgizar kasa ta ritsa da jama'a a kasashen Turkiyya da Syria inda aka tabbatar da mutuwar sama da mutane 44,000.
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan, ya sanar da cewa 'yan matsaloli aka samu amma an shawo kansu yayin da aka ceto mutane da dama.
Asali: Legit.ng