Yanzu-Yanzu: Dakarun kasar Siriya sun harbo jirgin yakin yahudawan Isra'ila
- Dakarun kasar Siriya sun harbo jirgin yakin yahudawan Isra'ila
- Sun samu nasarar harbo wani jirgin yakin yahudawan Isra'ila mai suna F-16
- Kasar ta Syria tuni ta bude wuta bayan Isra'ila ta yi mata "kutse".
Labarin da ke iso mana daga majiyar mu ya tabbatar mana da cewar dakarun sojojin kasar Siriya dake fama da rikikin yakin basasa na tsawon shekaru sun samu nasarar harbo wani jirgin yakin yahudawan Isra'ila mai suna F-16.
KU KARANTA: Saudiyya ta sake kashe wani dan dan Najeriya
To sai dai kamar yadda muka samu, matukan jirgin yakin su biyu sun samu nasarar fita daga cikinsa ta hanyar lema kafin ya fado a arewacin yankin na Isra'ila kamar dai yadda aka yi amannar cewa wannan ne karon farko da jirgin Isra'ila ya fado sakamakon rikicin na Syria.
Legit.ng ta samu cewa gwamnatin kasar ta Isra'ila ce ke ta kai hare-hare tun bayan da kasar Iran ta kaddamar da aike wa da jirage marasa matuka cikin Isra'ila din a lokutan baya.
Kafafen yada labarai na duniya dai sun bayyana cewa kasar ta Syria tuni ta bude wuta bayan Isra'ila ta yi mata "kutse".
A wani labarin kuma, Gwamnatin kasar Habasha watau Ethiopia a turance dake a kudancin Nahiyar Afirika ta bayyana kudurin ta na yafewa akalla fursunoni 746 cikin su kuwa hadda 'yan jarida, manyan jami'an gwamnati ta ake zargi da aikata laifukan ta'addanci da kuma cin amanar kasa da dai sauran su.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Antoni Janar na kasar ya bayar inda ya bayyana cewa wannan mataki da kasar ta dauka wajen rage zafafar siyasar kasar da kuma sauye-sauyen gwamnatin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng