Simon Ekpa: Shugaban Yan Ta'adda a Najeriya Ya Shiga Hannu, An Tura Shi Kurkuku

Simon Ekpa: Shugaban Yan Ta'adda a Najeriya Ya Shiga Hannu, An Tura Shi Kurkuku

  • Hukumomi a kasar Finland sun garƙame jagoran yan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biyafara a Kudancin Najeriya
  • An ruwaito cewa bayan gurfanar da Simon Ekpa, kotu ta tura shi kurkuku bisa laifin jagorantar ta'addanci a tarayyar Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa akwai karin mutane hudu da yan sandan Finland suka cafke tare da babban ɗan ta'addar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Finland - Rahotanni da suka fito daga kasar Finland sun tabbatar da cewa an cafke shugaban yan ta'addar Biyafara.

Simon Ekpa
An kama jagoran yan ta'adda a Finlad. Hoto: aduka Chinemelum Ogwueleka
Asali: UGC

Simon Ekpa ya zamo babban jagoran masu fafutukar kafa kasar Biyafara tun bayan kama Nnamdi Kanu a kasar Kenya.

Leadership ta wallafa cewa Simon Ekpa ya sha zuga matasa a Kudu maso Gabas su kai hari kan jami'an tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

'Tsaro a makarantu': Tinubu zai kashe N112bn a gagarumin aiki da ya tattago

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ekpa: An kama shugaban yan ta'adda

Bincike ya nuna cewa wata kotu a yankin Paijat Hame a kasar Finland ta daure ƙasurgumin ɗan ta'adda, Simon Ekpa.

An ruwaito cewa an kama Simon Ekpa ne bisa zargin jagorantar tayar da ƙayar baya a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Rundunar yan sandan Finland ta tabbatar da kama Ekpa tare da wasu mutane hudu a farkon makon da muke ciki.

"An kama babban wanda ake zargin ne saboda ingiza mutane su yi ta'addanci, sauran hudun kuma saboda ɗaukar nauyin ta'addanci.
An samu hadin kan kasa da kasa a yayin da ake bincike bayan kama mutanen."

- Yan sandan Finland

Daily Trust ta wallafa cewa Simon Ekpa ne ke ikirarin zama firaministan haramtacciyar kasar Biyafara.

Haka zalika dan ta'addar ne ya kawo tsarin zama a gida a jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya duk ranar Litinin.

Dama masana tsaro sun dade suna kira a kan kama dan ta'addar da sauran masu hura wutar rikici a Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

"Jama'a shaida ne:" Gwamnatin Tinubu ta ce ana fattakar 'yan ta'addan Lakurawa

Kanu: An bukaci a saki dan ta'adda

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rochas Okorocha ya buƙaci a roki shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saki Nnamdi Kanu.

Rochas Okorocha ya yi kira ne ga shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng