Yanzu-Yanzu: An kama Nnamdi Kanu shugaban IPOB, an dawo da shi Nigeria

Yanzu-Yanzu: An kama Nnamdi Kanu shugaban IPOB, an dawo da shi Nigeria

  • An kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar masu neman kafa Biyafara wato IPOB
  • Ministan shari'a, Mr Abubakar Malami ya tabbatarwa yan jarida cewa an dawo da shi Nigeria
  • Malami ya ce za a gurfanar da Kanu gaban babban kotu a Abuja don cigaba da masa shari'a

An kama shugaban kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Amma News Wire ta ruwaito cewa ministan shari'a kuma Attoni Janar, Abubakar Malami ya tabbatarwa da hakan yana mai cewa an kama shi ne ranar Lahadi 27 ga watan Yuni kuma an dawo da shi Nigeria ya fuskanci shari'a.

An kama Nnamadi Kanu, shugaban kungiyar IPOB
An kama Nnamadi Kanu, shugaban kungiyar IPOB. Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

KU KARANTA: Fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye birnin Kano

Ya ce an kama shi ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaron Nigeria da yan sandan kasa da kasa Interpol.

Malami ya kara da cewa za a gurfanar da Kanu a gaban alkali a babban kotun tarayya Abuja domin cigaba da shari'a da ake masa na tuhumar laifuka da suka shafi cin amanar kasa, mallakar bindiga ba tare da ka'ida ba da kafa kungiya ba bisa ka'ida ba.

Lokacin da aka fara kama Kanu

An fara kama shugaban na kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ne a watan Oktoban 2015 kan zargin hadin baki wurin aikata laifi da kasancewa mamba na haramtaciyar kungiya.

An bada belinsa kan dalilin rashin lafiya a watan Afrilu amma ba a sake ganinsa ba tun lokacin da sojoji suka kai samame gidansa watanni biyar bayan bada belin.

KU KARANTA: An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina

Kafa kungiyar ESN

A watan Disambar 2020, Kanu ya sanar da cewa ya kafa wata kungiyar tsaro na yankin kudu mai suna ESN. Daga bisani ya bawa gwamonin jihohin kudu wa'adin kwanaki 14 su haramta kiwo a fili.

Ya yi barazanar zai tura jami'an kungiyar ESN su tabbatar da dokar haramta kiwon idan gwamnonin ba za su yi hakan ba.

Rundunar sojojin kasan Nigeria da na sama, a watan Fabrairun wannan shekarar sun fara yi wa yan ESN dirar mikiya sakamakon hare-hare da yan kungiyar ke kaiwa hukumomin gwamnati.

A wani labarin daban, babban kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ta bada umurnin a ajiye mata shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu a hannun hukumar tsaron farin kaya DSS har zuwa ranar 26 ga watan Yuli, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton The Cable an kama Kanu ne a kasar waje aka dawo da shi Nigeria a jirgin sama a ranar Lahadi.

An sake gurfanar da shi gaban Mai shari'a Binta Nyako a ranar Talata.

Nyako ce alkalin da ta bada belinsa bisa rashin lafiya a shekarar 2017.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164