A Karshe, FBI Ta Kama Wanda Ya Shirya Harin Ta'addanci kan Sojojin Najeriya a Borno
- A wani sabon ci gaba da aka samu, hukumar FBI ta ce ta cafke Anas Said, wani dan Najeriya da ake zargin yana da alaka da ISIS
- Hukumar binciken manyan laifuffukan ta sanar da cewa ta cafke Anas a lokacin da yake shirin kai wani hari a birnin Houston
- A binciken da FBI ta yi, ta gano cewa Anas ne ya shirya harin ta'addanci da aka kai wa sojojin Najeriya a jihar Borno tun a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta sanar da kama Anas Said, wanda ake zargi da shirya harin ta’addanci kan sojojin Najeriya.
An rahoto cewa Anas Said ne ya kitsa yadda aka farmaki sojojin a shingensu na binciken ababen hawa da ke jihar Borno a shekarar 2023.
FBI ta cafke Anas a kasar Amurka
Kama Anas da FBI ta yi ya zama babban ci gaba wajen yaki da ta’addancin da ya shafi Najeriya da sauran kasashen duniya, a cewar rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
FBI ta bayyana cewa an kama Mista Anas a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Houston, Texas, yayin da ake zarginsa da shirin kai wani sabon hari na ta’addanci.
Ayyukansa sun ja hankalin duniya sosai, sakamakon alakar da ake zargin ya na da ita da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi na duniya.
Takardar tuhuma da aka shigar a kotun tarayya da ke Texas ta nuna cewa ana tuhumar Mista Anas Said da yunkurin safarar kayan aiki ga kungiyar ta'addancin ISIS.
Anas ya shirya harin kisan sojojin Najeriya
Hukumomi sun zargi cewa tun daga shekarar 2017 Mista Anas yake yada sakonni masu goyon bayan kungiyar ISIS a kafafen sada zumunta.
Takardun karar sun nuna cewa a watan Yulin shekarar 2022, Mista Anas ya wallafa bidiyon harin da aka kai kan sojojin Najeriya a wani shingen bincike a jihar Borno.
Anas ya wallafa wannan bidiyon a shafukan yanar gizo da ke da alaka da kungiyar ISIS.
Har yanzu ba a gano adadin sojojin Najeriya da suka rasa rayukansu a harin da ya auku a Borno ba, amma lamarin ya nuna tasirin ta’addanci kan sojojin kasar.
Hukuncin da ke jiran Anas Said
Baya ga zargin harin da ya kai a Najeriya, an kuma zargi Mista Anas da aikata laifuffukan ta’addanci a Siriya, musamman a biranen Damascus da Homs.
Idan aka same shi da laifi, Anas zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 a kurkuku tare da biyan tarar da za ta kai har $250,000.
Kamen ya haifar da ce-ce-ku-ce, amma rundunar sojojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa kan batun ba.
Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, bai amsa tambayoyin da jaridar Peoples Gazette ta yi masa kan lamarin ba.
An kama wanda ya shirya kisan sojoji
A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun Operation Hadin Kai sun kama Ba’ana Bdiya, wani 'tubabben dan Boko Haram' kan harin bam da ya kai ga halaka wasu sojoji.
An rahoto cewa Ba’ana Bdiya ya kai rahoton motsin sojojin ga 'yan ta'adda, wanda ya sa aka yiwa sojojin kwantan bauna a tare da tashin wasu daga cikinsu da bama-baman IED.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng