Sojojin Amurka sun kai hari kan 'yan bindigar arewacin Najeriya a kan Ba-Amurke guda daya
- Sojojin kasar Amurka sun gudanar da atisayen ceton ran wani Ba-Amurke da aka boye a arewacin Najeriya bayan an yi garkuwa da shi
- A ranar Talata ne 'yan bindiga suka sace Ba-Amurken a kasar Nijar tare da tsallakowa da shi zuwa Najeriya
- Kasar Amurka ta ce zata cigaba da kare 'yan kasarta da kuma manufofinta a ko ina a fadin duniya
Dakarun rundunar sojin kasar Amurka sun sanar da cewa sun kubutar da wani Ba-Amurke da 'yan bindiga suka boye a arewacin Najeriya bayan an yi garkuwa da shi a makon jiya.
A wani jawabi da kakakin gidan gwamnatin Amurka (Pentagon), Jonathan Hoffman, ya fitar, Amurka ta sanar da cewa dakarunta sun kai samamen ne da safiyar ranar Asabar.
A ranar Talata ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da wani Ba-Amurke a jamhuriyar Nijar tare da shigowa da shi Najeriya.
DUBA WANNAN: Sun kashe sojoji, sun kashe 'yan sanda - Wike ya zayyana irin barnar da IPOB suka yi a Ribas
"Dakarun rundunar sojin kasar Amurka sun gudanar da wani atisayen ceton rai da sanyin safiyar ranar 31 ga watan Oktoba a arewacin Najeriya. Sun kai samame maboyar 'yan bindiga domin kubutar da wani dan asalin kasar Amurka da aka yi garkuwa da shi," a cewar jawabin.
Jawabin ya kara da cewa; "sojojinmu sun yi nasarar kubutar da mutumin, wanda yanzu haka ya ke hannun jami'an bangaren tsaro na kasar Amurka. Babu wani sojan Amurka da ya rasa ransa yayin atisayen.
"Mu na mika godiya zuwa wurin kasashen da ke kawance da Amurka saboda goyon bayan da suka bamu wajen samun nasarar wannan atisaye.
DUBA WANNAN: Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi shagube a kan tsine mata a Masallatai
"Kasar Amurka za ta cigaba da kare 'yan kasarta da kuma manufofinta a ko ina, a fadin duniya."
A wani labarin da ya shafi 'yan bindigar arewacin Najeriya, Legit.ng Hausa ta wallafa cewa a kalla mutane goma aka sace a garin Dan Kurma dake jihar Zamfara bayan kashe mutu daya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng