An Shiga Tashin Hankali a Indiya, 'Yan Ta'adda Sun Harbe Tsohon Minista har Lahira

An Shiga Tashin Hankali a Indiya, 'Yan Ta'adda Sun Harbe Tsohon Minista har Lahira

  • Wasu da ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne sun harbe wani babban dan siyasar Indiya mai suna Baba Siddique a Mumbai ranar Asabar
  • Dan majalisar mai shekaru 66 a duniya ya taba rike mukamin minista a jihar Maharashtra da ke yammacin kasar kuma ya yi fice
  • An harbe Baba Siddique babu adadi a kirjinsa a wajen ofishin dansa, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar Indiya suka ruwaito

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Indiya - An harbe wani babban dan siyasa a Mumbai, babban birnin hada-hadar kudi na Indiya ranar Asabar, makonni gabanin zabukan jihohi.

An rahoto cewa 'yan sandan Indiya sun fara bincike kan wannan kisan yayin da ake zargin wani gungun 'yan ta'adda da aikata laifin.

Kara karanta wannan

Yan daba sun harbi shahararren ɗan TikTok, sun sace masa gwala gwalai

'Yan ta'adda sun harbe tsohon ministan Indiya har lahira
'Yan ta'adda sun kashe tsohon minista a Indiya ana makonni da zaben jihohi. Hoto: @BabaSiddique
Asali: Twitter

An harbe tsohon ministan Indiya

An ce dan siyasar, Baba Siddique mai shekaru 66 ya taba zama minista a jihar Maharashtra da ke yammacin kasar kuma an harbe shi ba adadi a kirji, inji rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafafen yada labarai na Indiya sun ruwaito cewa an harbi tsohon ministan ne a wajen ofishin dansa a Mumbai.

Mataimakin babban ministan Maharashtra, Ajit Pawar, daga jam'iyyar da Siddique ya ke ya ce "ya kadu" da "harin kisan gillar".

An cafke wasu da ake zargi

Jaridar Hindustan Times ta rawaito cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargi da kai harin, kuma ‘yan sanda na neman wani da ya tsere.

Tashar watsa labarai ta NDTV ta ce mutanen biyun sun yi ikirarin cewa suna cikin wata kungiyar Lawrence Bishnoi, wanda ke tsare a gidan yari kan zargin aikata kisa da dama.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Harbin na zuwa ne makonni kadan bayan da aka inganta tsaron Siddique bayan da aka yi masa barazanar kisa, da kuma gabanin zaben da za a yi a karshen wannan shekara.

An harbe minista har lahira

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani minista a kasar Uganda ya gamu da ajalinsa bayan sojan da ya ke tsaron lafiyarsa, ya bindige shi har lahira.

An ce an kashe karamin ministan kwadago, samar da ayyukan yi da harkokin masana'antu na kasar Uganda, Kanal Charles Okello Engola a ranar 2 ga watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.