'Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 6 da Suka Bude Caji Ofis din Bogi Tsawon Wata 8

'Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 6 da Suka Bude Caji Ofis din Bogi Tsawon Wata 8

  • Rundunar 'yan sandan kasar Indiya sun yi ram da wasu mutane 6 da suke 'yan sandan bogi kuma suka bude caji ofis din bogi a kasar
  • Mutanen da suka kunshi maza 4 da mata 2, suna karbar korafin jama'a da karbe kudadensu kan zasu kwatar musu hakki, inshorar gidaje ko samar musu da aikin 'yan sanda
  • Sun kawata caji ofis din da bindigogin gargajiya, lambar yabo da kayan 'yan sandan na asali, amma shugabansu ya arce ba a kama shi ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jami'an 'yan sanda a kasar Indiya sun cafke wasu mutane shida da suka dauka tsawon watannin takwas a matsayin 'yan sandan bogi.

Ba a nan mutum shidan suka tsaya ba, sun bude caji ofis na bogi a wani otal inda suke karbe kudaden mutane hankali kwance, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shiga siyasa: Matasa a Abuja sun kama wani Bishap, sun lakada masa dukan tsiya

'Yan sandan bogin sun hada baki da wasu maza hudu ne da mata biyu kuma an kama su duk da shugaban wannan damfarar ya arce ba a gan shi ba.

Caji Ofis din Bogi
'Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 6 da Suka Bude Caji Ofis din Bogi Tsawon Wata 8. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

'Yan sandan bogi ba sabon abu bane a kasar Indiya, amma a wannan za a iya cewa shine na farko da aka samu masu bude caji ofis gaba daya suna karbar korafin mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Srivastava, shugaban rundunar 'yan sandan kasar ya sanar da manema labarai cewa, 'yan sandan bogin sun bude caji ofis din a jihar Bihar, wurin da ba kai tazarar mita 500 ba daga shugaban shugaban rundunar 'yan sandan.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, an samu bindigogin gargajiya da lambobin yabo gami da kayan 'yan sanda na gaske a wurin.

Hakazalika, basu yi kasa a guiwa ba, suna amshe kudaden jama'a da sunan zasu kwato musu hakkinsu, ko inshorar gidaje, ko samar musu da aikin 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun tarfa jigon APC a yankinsu, sun hallakashi

Har ila yau, suna biyan Rufi 500 ga jama'ar anguwa. Dubunsu dai ta cika ne yayin da 'yan sandan kasar suka hangesu da bindigun gargajiya a madadanin na zamani da aka san 'yan sandan da su.

Yadda Matukan Jirgin Sama Suka Bingire da Bacci Suna Tsaka da Tuka Fasinjoji

A wani labari na daban, matukan jirgin sama har su biyu sun bingire da bacci, hakan yasa ba su sauka da wuri ba a yayin da suka kwaso fasinjoji daga Sudan zuwa kasar Habasha a ranar Litinin, kamar yadda rahoton Aviation Herald ta bayyana.

Lamarin ya faru ne a jirgin Kamfanin Ethiopian Airlines mai lamba 737-800 wanda ya taso daga Khartoum zai je Addis Ababa, jaridar Leadership ta rahoto.

Bayanai da aka samu daga shafin yanar gizon ya bayyana cewa, jirgin na tafe ne da nisan kafa 37,000 lokacin da ya gaza sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Addis Ababa Bole inda zai sauka a ranar 15 ga watan Augusta.

Kara karanta wannan

Yadda Shehin Malami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi

Asali: Legit.ng

Online view pixel