Jadawali: Jerin Biranen Afrika 10 Mafi bunkasa a Yawan Jama'a, Abuja Ce Ta 9

Jadawali: Jerin Biranen Afrika 10 Mafi bunkasa a Yawan Jama'a, Abuja Ce Ta 9

A halin yanzu, manyan biranen kasashen Afrika suna samun ci gaban da ba a ga irinsa a baya ba, hakan ya haifar da wayewa, habakar tattalin arziki, da masu saka hannun jari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A cikin jadawalin 2024, Global Firepower ta bayyana cewa Alkahira da ke kasar Masar ce babban birni mafi yawan jama'a a Afrika, inda suke da mazauna miliyan 21.75.

Jerin biranen Afrika 10 mafi yawan jama'a a 2024
Alkahira da wasu biranen kasashen Afrika mafi yawan jama'a. Hoto: Peeterv, Mtcurado, Angel Villalba
Asali: Getty Images

Kinshasa da ke Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, da Luanda, na Angola, suna bin juna da mutane miliyan 15.628 da miliyan 8.952, bi da bi, inji rahoton Tribune.

Ga jerin manyan biranen Afrika guda 10 bisa yawan jama'a:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya koka da karuwar talauci a Arewa duk da yan siyasarta na gwamnati

1. Alkahira, Masar

Mutanen Masar a halin yanzu sun kai 117,005,320 bisa la'akari da rahoton Worldometer da ya samu daga Majalisar Dinkin Duniya, inda birnin Alkahira ke da mutane 21,750,000.

2. Kinshasa, Kongo

An kiyasta yawan jama'ar Kinshasa a shekarar 2024 ya kai 17,032,300. Rahoto ya nuna cewa a shekarar 1950, mutane 201,905 ne kacal a birnin Kinshasa.

3. Luanda, Angola

Luanda, babban birnin Angola, birni ne mai tashar jiragen ruwa a yammacin gabar tekun Kudancin Afirka.

Yawan mutanen birnin Luanda a shekarar 2024 ya kai 9,651,000, karuwar kashi 3.86 daga 2023.

4. Khartoum, Sudan

Yawan mutanen Khartoum, babban birnin kasar Sudan a shekarar 2023 ya kai 6,344,000, karuwar kashi 2.99 daga 2022. Khartoum birni ne da ke Kudu da kogunan Blue da White Nile.

5. Addis Ababa, Ethiopia

Addis Ababa babban birni ne kuma birni mafi girma a kasar Habasha. A ƙidayar jama'a ta 2007, an ƙiyasta yawan mutanen birnin Addis Ababa ya kai 2,739,551.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Yobe, sufetan 'yan sanda ya kashe wani mutumi kan N200

6. Nairobi, Kenya

Nairobi, babban birnin Kenya na da yawan mutanen da suka kai 5,541,170 a 2024. An samo sunan Nairobi daga kalmar Maasai, 'Enkare Nairobi', wanda ke nufin 'gari mai sanyin ruwa'.

7. Yaoundé, Kamaru

Yaoundé babban birnin kasar Kamaru ne, kuma mutanen cikinsa sun kai kimanin 4,681,770, birni na biyu mafi girma a kasar bayan birnin Douala mai tashar jiragen ruwa.

8. Kampala, Uganda

An kiyasta yawan jama'ar Kampala a shekarar 2024 zuwa 4,050,830. Babban birnin Uganda na da iyaka da tafkin Victoria, tafkin mafi girma a Afirka.

9. Abuja, Najeriya

Abuja babban birnin Najeriya ne da ke a tsakiyar kasar. An kiyasta cewa yawan mutanen Abuja ya kai 4,025,740. Dutsen Aso Rock ne ya mamaye sararin samaniyar Abuja.

10. Dakar, Senegal

Dakar babban birnin kasar Senegal ne, a yammacin Afirka. Dakar birni ne mai tashar jiragen ruwa ta Atlantika kuma ya na yawan mutanen da suka kai 3,540,000.

Kara karanta wannan

NiMet: Za a zabga ruwan sama daga Laraba zuwa Juma'a a wasu jihohin Arewa 16

Kasashen Afrika mafi karbar rashawa

A wani labarin, mun rahoto cewa cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a duniya, inda ya yi katutu a wasu kasashen Afrika, kamar yadda kididdigar 2023 ta nuna.

Rahoton ya nuna cewa cin hanci da rashawa ya yi kamari a kasar Somaliya saboda tashe-tashen hankulan siyasa da kuma rikice-rikicen da ke faruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.