Ethiopia: Abubuwa 5 game da kasar da ta fara karbar Musulunci, ba a yi mata mulkin mallaka ba
- Kasar Ethiopia ita ce kasar da ta fara karbar addinin Musulnci a duniya bayan ta bai wa Annabi Muhammadu masauki
- An gano cewa ba a taba yi wa kasar mulkin mallaka ba kuma zaratan sojojinsu na yakar makiya tare da zakuna, damisa da kudan zuma
- Kasar gabashin Afrikan ta mallaki wurin da ya fi ko ina zafi a duniya kuma ta na da wani tafki da ke amon wuta akai-akai
Ethiopia ta shiga cikin jerin kasashen duniya da Turawa ba su taba yi musu mulkin mallaka ba tun farkonsu.
Kasar ta nan a nahiyar Afrika, za mu iya cewa su biyu ne rak a nahiyar tare da kasar Liberia wadanda ba a taba yi wa mulkin mallaka ba.
Baya da wannan al'amarin, kasar da ke gabashin nahiyar Afrika ta na da labarai masu bada al'ajabi da tarihi masu bada mamaki.
'Yan sanda za su gurfanar da wata matashiya ‘yar shekara 25 da ke yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Katsina
Legit.ng ta tattaro muku abubuwa biyar game da kasar da sojojin ta ke yakar makiya tare da miyagun dabbobi kamar su Zakuna, kudan zuma, giwaye da damisa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Ethiopia ce kasa ta farko a duniya da ta fara karbar Musulunci
Kasar an gano ita ce ta farko a duniya da ta fara karbar Musulunci a matsayin addini.
Kamar yadda Mo Afrika Tours ta sanar, kasar an gano ta bai wa Annabi Muhammad S. A. W, iyalansa da wasu mabiyansa masauki yayin da ya ke fuskantar kalubale daga masu bautar gumaka.
A lokacin kuwa, kashi 35 na jama'ar kasar mabiya addinin Islama ne.
2. Dallol a Ethiopia shi ne wuri mafi zafi a fadin duniya.
Kamar yadda masana suka gano, matsakaicin dumin Dallol da ke kasar ya kai 35°C (95°F) a tsakanin 1960 da 1966.
Babu shakka Dallol da ke Danakil a kasar Ethiopia shi ne wuri mafi zafi a fadin duniya, Absolute Ethiopia ta ruwaito hakan.
3. Akwai sama da yarika 80 da ake yi a kasar Ethiopia
Kasar Ethiopia ta kasance kasa ce mai yarika masu yawa. Jama'ar kasar na yin yarika sama da 80
Big Seven Travel ta ruwaito cewa, ana yin yarika da suka hada da Oromo, Amharic, Somali da Tigrinya.
Sai dai a bangaren koyarwa da ilimi na kasar, ana amfani da yarin Ingilishi ne.
4. Ethiopia ta na da tafki mai amon wuta wanda jama'a ke cewa hanya ce zuwa wutar Jahannama
Erta Ale da ke kasar shi ne tafki mai amon wuta mafi dadewa da aka taba samu a duniya.
Absolute Ethiopia ta ce tafkin ya kasance tun daga 1906. An san shi da zafi kuma ya na daya daga cikin wuri da ke amon wuta sosai a duniya.
5. An fara samun Coffee a kasar Ethiopia
Coffee wanda a yanzu duniya ake amfani da shi sosai ya fara ne daga kasar Ethiopia, Absolute Ethiopia ta ruwaito.
Yayin da babu wani bayani gamsasshe da duniya ta yarda da shi na cewa a kasar aka fara samun shi, an yadda cewa an fara diban shi ana kai shi wasu sassa na duniya ne ta hanyar safarar bayi da sauransu.
Asali: Legit.ng