Amurka Ta Cafke Dan Najeriya kan Zambar $10m, Yana Fuskantar Daurin Shekara 20

Amurka Ta Cafke Dan Najeriya kan Zambar $10m, Yana Fuskantar Daurin Shekara 20

  • An kama Yomi Jones Olayeye, wani dan Najeriya dan a filin jirgin sama na John F. Kennedy, kuma yana fuskantar tuhumar zamba
  • Ana zargin Yomi da abokan harkallarsa da yin amfani da bayanan sata wajen damfarar shirye-shiryen ba da tallafi har guda uku
  • Amurka ta ce idan aka same shi da laifi, Yomi zai fuskanci zaman gidan yari na tsawon shekaru 20 da tarar dalar Amurka 250,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Gwamnatin kasar Amurka ta cafke wani dan Najeriya, Yomi Olayeye kan zargin ya karkatar da $10m na tallafin COVID-19 da aka baiwa marasa aikin yi a Amurka.

Ana tuhumar Yomi Olayeye da aikata laifuffuka da suka shafi hada baki, satar kudi ta intanet da kuma satar bayanai.

Kara karanta wannan

An cafke masu kaiwa 'yan bindiga makamai a Arewa, 'yan sanda sun yi bayani

Ofishin shari'a na Amurka ya yi magana kan kama wani dan Najeriya
'Yan sandan Amurka sun kama wani dan Najeriya bisa zargin aikata zamba. Hoto: @Naija_PR
Asali: Twitter

Ofishin Antoni Janar na Amurka da ke gundumar Massachusetts, karkashin ofishin shari'a na kasar ne ya fitar da sanarwar hakan a shafinsa na yanar gizo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa an kama Mista Yomi a ranar 13 ga watan Agusta a lokacin da ya dura filin jiragen sama na John F. Kennedy da ke New York.

An cafke dan Najeriya a Amurka

Sanarwar ta kara da cewa:

"Mista Yomi da wasu da ake zargi sun tafka damfara a wasu shirye-shirye guda uku na ayyukan jin kai da ma'aikatar taimakawa marasa aikin yi ta Massachusetts ke gudanarwa."
"An yi zargin sun yi amfani da bayanan sirri na sata domin neman tallafi na rashin aikin yi a jihohi da yawa, ciki har da Massachusetts, Hawaii, da Indiana."

Hukuncin da zai iya fuskanta a Amurka

A cewar ofishin shari'a na Amurka:

Kara karanta wannan

Airbus A330: Abin da ya kamata ku sani game da sabon jirgin shugaban kasar Najeriya

“A dunkule, Yomi da abokan harkallarsa da ake zargin sun nemi tallafin akalla $10m daga hukumomin inshora na UI, PUA da FPUC kuma sun karbi sama da $1.5m."

Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta kuma bayyana cewa, idan aka same shi da laifi, Yomi zai fuskanci zaman gidan yari na tsawon shekaru 20 da tarar dalar Amurka 250,000.

Amurka za ta ba Najeriya tallafin $27m

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta sanar da cewa Najeriya za ta samu $27m (N42.9bn) a wani bangare na tallafin $536m da za ta ba kasashen Afrika.

Kasar Amurka ta ce wannan tallafin wani bangare ne na kudurin kasarta na ba da taimako ga mutane marasa galihu da kuma kasashe masu karbar baki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.