Amurka ta haramta ma Najeriya mika $100m daga kudin Abacha ga gwamnan jahar Kebbi

Amurka ta haramta ma Najeriya mika $100m daga kudin Abacha ga gwamnan jahar Kebbi

Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana rashin amincewarta da shirin gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari na ware zunzurutun kudi dala miliyan 100 daga kudaden Abacha tare da mikasu ga gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu.

Jaridar Guardian ta ruwaito sashin shari’a na kasar Amurka ya bayyana Bagudu daga cikin wadanda suke da hannu a badakalar satar kudi da rashawa a gwamnatin tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha.

KU KARANTA: Za mu ga bayan Boko Haram da ikon Allah – Sultan ya baiwa yan Najeriya tabbaci

Sashin sharia’r ta bayyana Najeriyana kawo ma gwamnatin kasar Amurka tasgaro gae da kokarinta na kwato kudaden Abacha da aka sace ta hannun Bagudu, daga cikin kudden akwai biliyoyi da ta zargi Bagudu da yaron Abacha, Muhammed suka suka kwashe daga Najeriya zuwa kasar Amurka ta amfani da asusun bankuna.

Don haka Amurka ta bukaci Najeriya ta janye karar da ta shigar a kotun kasar Birtaniya, shari’ar dake kawo ma Amurka cikas wajen kwato wadannan kudaden domin amfanin yan Najeriya, saboda a cewar Amuka, akwai wata yarjejeniya da ta kai shekara 17 da ta mallaka ma Bagudu kudaden.

Wani tsohon jami’in hukumar leken asiri na kasar Amurka, Mathew Page ya bayyana cewa a maimakon gwamnatin Najeriya ta yi maraba da kokarin da kasar Amurka take yi wajen kwato wadannan kudade tare da bata hadin kai, sai ma ta koma tana goyon bayan iyalan Abachan.

Zuwa yanzu, Najeriya ta kwato fiye da dala biliyan biyu na kudaden Abacha tun bayan mutuwarsa, shi kuwa Bagudu, a shekarar 2013 gwamnatin Amurka ta fara kokarin kwato wasu kadarorinsu da suke birnin Landan.

A wani labarin kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma shugaban majalisar koli ta Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya baiwa yan Najeriya tabbacin Najeriya za ta samu nasara a yakin da take yi da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram duk da halin da ake ciki.

Sultan ya bayyana haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin taron kasa da kasa a kan soyayya da zaman tare karo na 5, wanda aka yi ma taken “Yaki da zafin ra’ayi don samar da zaman lafiya” da gidauniyar UFUK Dialogue ta shirya.

Sultan, wanda ya samu wakilcin Sarkin Jiwa, Dakta Idris Musa ya bayyana cewa yawancin yan Najeriya basu kaunar junansu, sa’annan ya koka kan kashe kashe da zubar da jini da ake yi a Najeriya, inda yace matsalar ta kai ga mai kudi yana gudun talaka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel