Cikakken Jerin Sunaye da Bayanan Kasashe 10 da Suka fi Samar da Zinare a Afirka
Zinare ya samu gurbin zama a matsayin kadara wanda darajarsa kullum ke kara hauhawa a duniya inda farashinsa ya kai $2,468.40 kan kowanne giram 31 a Yunin 2024.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Afirka tana da wasu manyan wuraren ajiyar zinari a duniya, inda kowace kasa daga cikin kasashe masu wuraren ajiyar ke riƙe da sama da tan 100 na zinare.
A cewar majalisar harkokin zinare ta Duniya (WGC), yawan zinare da ake samarwa a duniya ya karu a cikin shekaru hudu da suka gabata, wanda ya karu da kashi 12.
Samar da zinare ya bunkasa a duniya
Binciken yanayin kasa na Amurka ya bayyana cewa adadin zinare da ake samarwa a duniya ya kai tan 3,000 (MT) a bara (2023).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A harkar hako zinari a duniya ba a bar nahiyar Afrika ba domin an ce yammacin Afirka na daya daga cikin yankuna mafi saurin bunkasuwa a duniya wajen samar da zinari.
Rahotan mujallar kasuwanci ta Business Insider ya bayyana cewa yammacin Afrika ne tushen kusan rabin zinaren da ake samarwa a Afirka a halin yanzu.
Kasashe 10 mafi samar da zinare a Afirka
Bayanai daga jaridar Vanguard sun yi nuni da kasashen Afirka da suka fi samar da zinari daga 2010 zuwa yau:
1. Ghana ce tushen samar da zinare
Wanda tarihi ya fi sani da "Tushen Zinare," Ghana ta kasance tana hako zinare tun karni na 15. An ce masa'antar ce ke samar da kashi 40 na duk abin da kasar take samu a daga kasuwancin waje.
2. Zinare ne aka fi fitarwa waje a Mali
An ce zinare shi ne abin da kasar Mali ta fi fitarwa inda ya zama shi ke da kaso 80 na duk kayayyakin da take fitarwa a 2023.
Hakazalika, ma'aikatar hako ma'adanan Mali ta samar da ton 800 a rumbun ajiya, sai ton miliyan biyu na 'iron ore,' ton 5,000 na 'uranium,' don miliyan 20 na 'manganese,' ton miliyan hudu na 'lithium da ton miliyan 10 na 'limestone.'
3. 'Birnin Zinare' na kasar Afrika ta Kudu
A shekara ta 1975, Afirka ta Kudu ta samar da kashi 40 cikin 100 na zinaren duniya, amma a yau ita ce ke da kashi 4.2 na abin da ake hakowa a duniya.
Duk da wannan koma bayan, masana'antar hakar zinare ta ƙasar, wacce ta fara aiki a ƙarni na 19, ta taka muhimmiyar rawa a ci gaban Johannesburg, inda aka fi sani da eGoli, "Birnin Zinari."
4. Burkina Faso ta gina matatar zinare
A cewar kungiyar fayyace masana'antu ta EITI, bangaren ma'adinai ke ba da kashi 14.3 na kudaden shiga na kasar Burkina Faso.
Duk da haka, yawan zinari da ake samarwa a kasar ya ragu daga tan 66.8 a shekarar 2021 zuwa tan 57.6 a shekarar 2022, raguwar kashi 13.7.
A martanin da gwamnatin soji ta Burkina Faso a shekarar 2023, ta fara gina matatar zinare ta farko a kasar, wanda za ta samar da kusan kilogiram 400 na zinari a kowace rana.
Sudan ta fara bunkasa a ma'adanai
Duk da cewa har yanzu rainon yawancin ma'adinan Sudan ake yi, sai dai hakar ma'adinai ke samar da kusan kashi 4 na arzikin kasar, inda zinari ya zama ja gaba a wannan fanni.
Sauran kasashen Afrika mafi hako zinare
Lamba | Sunan kasa | Yawan zinare (tan) |
6. | Guinea | 64.9 |
7. | Tanzaniya | 52 |
8. | Côte d'Ivoire | 51.5 |
9. | Zimbabwe | 46.6 |
10. | Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo | 45.4 |
Meyasa babu Najeriya a jadawalin?
Rashin Najeriya (wanda ke da kaso kusan 0.5 na yawan zinari a duniya) daga cikin jerin ya faru daga nauyin da gwamnati ta yi na shiga kasuwar hako ma'adinai.
A cewar kafar bincike ta Agusto, gwamnatin Najeriya ta fara samun manyan ci gaba a harkar hakar zinare a shekarar 2009.
Tare da kiyasin arzikin zinare na Najeriya ya kai oz 757,000, kuma darajarsa ta kai dala biliyan 1.4, akwai fatan farfado da masana'antu da kuma kara yawan kasuwar samar da zinare ta duniya.
Dan Najeriya ya gano mahakar zinare
A wani labarin, mun ruwaito cewa Mahdi Shehu, mai sharhi kan al'amuran jama'a ya fallasa wani haramtaccen wurin hakar zinare a wani kauye a jihar Zamfara.
Mai rajjin kare hakkin dan adam din ya kuma saki wani faifan bidiyo da ke nuna ma'aikatan da ke aikin hakar zinare a yayin da ya ce wurin hakar zinaren mallakin wani babban dan siyasa ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng