Ku kalli yadda ake hako zinare a Arewa (Hotuna)
- Ministan ma'adanai na Najeriya watau Mr kayode Fayemi ya ziyarci inda ake hako ma'adanai musamman ma Zinare a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya.
- A lokacin ziyarar tasa, Ministan yace: "Tabbas wannan gwamnatin da shugaba Buhari yake jagoranta tana da kyawawan manufofi musamman ma ga masu hakar ma'adanai na kasar nan."
Har ila yau a lokacin ziyarar tasa, ministan ya kuma je inda ake hakar ma'adanan ba bisa ka'ida ba duk dai a jihar ta Kaduna a cikin karamar hukumar Birnin Gwari.
A wani labarin kuma, Shugaban sashen nazarin harkokin cigaba na jami'ar Ibrahim Badamasi Babaginda (IBB) dake a karamar hukumar Lapai ta jihar Niger Prof. Nuhu Obaje ya sanar da samun danyen mai a yankin tekun Bida.
Farfesa Nuhu ya sanar da cewa sashen manazartan da yake jagoranta sun gano tarin danyen mai mai yawan gaske a yankin na tekun Bida duk dai a cikin jihar ta Niger a wani bincike da suka yi.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng