Jami'an tsaron Najeriya sun kama mutane 6 masu hako zinare ta haramtacciyar hanya a Arewa
Jami'an rundunar hukumar tsaron nan ta al'ummar farar hula watau Civil Defence a turance ta bayar da sanarwar kama wasu gungun mutane da take zargi da laifin hakar ma'adanin zinare ta haramtacciyar hanya a karamar hukumar Minna babban birnin jihar Neja.
Kwamandan rundunar ta jami'an tsaron na Sibil defence a jihar mai suna Mista Philip Ayuba shene ya shaidawa yan jarida hakan a ofishin sa dake a hedikwatar rundunar a kan titin tunawa da marigayi Mandela a Minna din.
Legit.ng ta samu kuma cewa hukumar tasu tana da alhaki akan dukkan yan Najeriya da su tabbatar da bin doka da oda sannan kuma ya bayyana kamasu a matsayin anunda ya yazama dole don samun ingattacen tsaro ga alummar yankin.
Daga karshe kuma kwamandan rundunar dai Mista Ayuba yace da zarar sun gama binciken su to tabbas za su turasu wadanda take zargin kotu domin shari'a.
Asali: Legit.ng