An bayyana Sheikh Ibrahim Saleh a matsayin mutum na 2 a duniya da yafi kowa ilimin Hadisi
- Sheikh Ibrahim Saleh ne ya bayyana a na farko a nahiyar Afirka kuma na biyu a fadin duniya a ilimin hadisi
- Babban malamin dan asalin jihar Borno ne kuma ruwa biyu ne daga iyaye ‘yan Maiduguri da Shuwa Arab
- Malamin babban makusanci ne ga Sheikh Abubakar Elmiskin da Shiekh Abdul Fathi
Sheikh Ibrahim Saleh ne ya bayyana a na daya a ilimin hadisi a nahiyar Afirka, amma na biyu a fadin duniya baki daya. Malamin masani ne babba a ilimin hadisi a wannan zamani.
Sheikh Ibrahim Saleh asalin dan Kanem-Bornu ne.
A wata tattaunawa da aka yi da malamin da harshen Kanuri a wani gidan rediyo da ke Maiduguri, Malamin ya bayyana cewa shi ruwa biyu ne.
Ya ce iyayen shi daya kabilar Kanuri ne dayan kuma Shuwa Arab. A tattaunawar da aka yi da Ibrahim Saleh, ya iya yaren Kanuri sosai ba kadan ba. A takaice dai, mutane da yawa suna cewa yaren Kanuri na daya daga cikin yarikan da ya iya.
An haifa Sheikh Ibrahim Saleh a jihar Borno a yankin Arewa maso gabas ta Najeriya. Yana magana da Larabci, Kanuri, Turanci da kuma Hausa.
Babban aboki ne kuma makusanci ga Sheikh Abubakar Elmiskin da Sheikh Abdul Fathi. Babban shehin malami ne na darikar Tijjaniya Wal Faidatul Ibrahimiya a duniya.
Muna matukar takama dashi tare da mishi fatan Allah ya ci gaba da shige mishi gaba da mishi albarka. Ameen
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng