An yi Rashi a Duniyar Kwallon Kafa, Tsohon Shugaban Hukumar CAF, Issa Hayatou Ya Rasu
- Issa Hayatou wanda ya dade yana shugabantar hukumar kwallon kafar Afirka (CAF) ya rasu ana saura kwana daya ya cika shekara 78
- Marigayin wanda aka haifa a shekara ta 1946, ya kasance mutum mai kima wanda ya bar tarihi a harkar wasanni musamman kwallon kafa
- Dan Kamarun ya rike mukamin mukaddashin shugaban hukumar FIFA daga 2015 zuwa 2016 bayan rike shugaban CAF na shekaru 29
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kamaru - An ruwaito cewa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afirka, Issa Hayatou ya rasu a ranar Alhamis bayan ya sha fama da rashin lafiya.
A gobe Juma'a, 9 ga watan Agusta ne Issa Hayatou ke cika shekara 78 a duniya.
Mukaman da Isaa Hayatou ya rike
Dan Kamarun ya kasance shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) na tsawon shekaru 29 daga 1988 har zuwa lokacin da aka sauke shi a 2017, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma rike mukamin mukaddashin shugaban hukumar FIFA daga 2015 zuwa 2016 bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya ta dakatar da Sepp Blatter.
Issa Hayatou, wanda dan uwansa ne Firaministan kasar Kamaru, ya kasance mai kula da harkokin wasanni a tsawon rayuwarsa.
An zargi Issa Hayatou da cin hanci
An ce Issa Hayatou ya kasance 'dan kwamitin gasar Olympics na duniya daga 2001-2016, bayan haka ne kuma ya zama mamba na girmamawa.
Jaridar TRT ta rahoto cewa a shekarar 2011 hukumar IOC ta hukunta Issah Hayatou bisa rawar da ya taka a badakalar cin hanci da rashawa a hukumar ta FIFA.
An yi masa tsawatarwa bayan da BBC Panorama ta yi ikirarin cewa ya karbi kusan dala 20,000 daga rusasshiyar kamfanin tallan wasanni na ISL a shekarar 1995.
Isaa Hayatou ya musanta karbar cin hanci da rashawa kuma ya ce kudaden kyauta ne ga hukumarsa.
Fadi tashin Isaa Hayatou
Zamansa a shugabancin hukumar kwallon kafa ta Afirka ya sa wasan kwallo ya samu ci gaba duk da cewa ana zargin Hayatou da jan kafa wajen kawo sabbin sauye-sauye.
Hayatou ya kalubalanci Blatter a matsayin shugaban FIFA a shekara ta 2002, amma ya sha kaye yayin da kasashen Afirka da dama suka yi watsi da shi a kuri'ar adawa da Swiss.
Tsohon dan wasan Arsenal ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Kevin Campbell ya rasu a ranar Asabar 15 ga watan Yuni bayan fama da jinya.
Dan wasan gaba, Campbell ya taka leda a gasar Premier a Arsenal, Nottingham Forest, Everton da kuma West Bromwich Albion.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng