Hukumar FIFA ta amince da canjin yan wasa 5 yayin wasan kwallon kafa
Daga yanzu kungiyoyin kwallon kafa za su iya sauya yan wasa har guda biyar a wasan kwallon kafa, kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta ayyana.
Kamfanin dillancin labarun AFP ta FIFA ta sanar da haka ne a ranar Juma’a, inda tace dokar za ta fara aiki ne da zarar an koma harkar kwallo bayan an shawo kan annobar Coronavirus.
KU KARANTA: Makashin maza: Sojoji sun halaka ‘Orjondu’ da suka dade suna farautarsa wurjanjan a Benuwe
Sanin kowa ne a wasan kwallon kafa yan wasa 3 kadai kungiyoyin kwallon kafa suke da daman canzawa, amma wannan sabuwar dokar za ta taimaka ma yan wasa sosai.
FIFA ta ce dalilin wannan doka shine a kokarinsu na cike gibin da suka bari sakamakon hutun da aka tafi, kungiyoyi zasu yi fama da wasanni da dayawa idan aka koma harkar kwallo.
Don haka hutun da aka yi zai shafi kuzarin yan wasa da lafiyarsu, don haka dole a kare su da wannan doka, haka zalika za’a dakatar da amfani da na’aurar VAR na dan wani lokaci.
“Ko da yake an amince ma kungiyoyi su canza yan wasa 5, amma don gudun yamutsa wasan, kungiyoyi zasu samu daman canza yan wasa uku ne kadai a cikin wasa, sai idan an kai lokacin kari na Extra time, shi ne zasu iya kara canza yan wasa biyu.
“Haka zalika ganin daman masu shirya gasar kwallon kafa a ko ina ne su dabbaka wannan dokar ko kuma a’a, dokar za ta yi aiki ne a gasar da za’a kammala zuwa 31 ga watan Disamba, amma FIFA za ta duba yiwuwar kara wa’adinsa.” Inji sanarwar.
Sai dai zuwa yanzu babu tabbacin ko dokar za ta zama ta dindindin, amma idan aka yi haka, manyan kungiyoyi masu kwararrun yan kwallo da yawa ne zasu fi cin moriyarta.
A wani labarin kuma, za'a koma gasar Bundesliga ta kasar Jamus kafin karshen watan Mayu, yayin da gasar Firimiya ta kasar Ingila ake cigaba da duba yiwuwar ranar komawa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng