InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Mai Gadin Ka'abah na 109 a Makkah
- Addinin Musulunci ya yi babban rashi bayan dadadden mai gadin Ka'abah ya riga mu gidan gaskiya a birnin Makkah
- Marigayin Dakta Saleh Bin Zain Al-Shaiba shi ne mai kula da makullin Ka'abah na 109 a tarihin Musulunci
- Tuni aka yi sallar jana'izarsa a Masallacin Harami tare da binne shi a makabartar Al Mualla a yau Asabar 22 ga watan Yunin 2024
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Makkah, Sa'udiyya - An shiga jimami bayan rasuwar mai gadin Ka'abah da ke kasar Saudiyya.
Marigayin Dakta Saleh Bin Zain Al-Shaibi ya rasu ne da safiyar yau Asabar 22 ga watan Yunin 2024.
Al-Shaiba: An yi jana'izarsa a Masallacin Harami
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Inside The Haramain ta wallafa a shafin X da safiyar yau Asabar 22 ga Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin rasuwarsa, Al-Shaibi shi ne mai rike da makullin Ka'abah da kula da ita na 109 a tarihi.
Tuni aka gudanar da sallar jana'izarsa a Masallacin Harami a yau Asabar 22 ga watan Yunin 2024.
Har ila yau, bayan sallar jana'izarsa an binne shi a makabartar Al Mualla da ke birnin Makkah a Saudiyya.
Kamar yadda rahoton ya tabbatar zaben mai gadin zai ci gaba da zuwa daga iyalan Al-Shaiba kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya umarta.
Mai gadin kabarin Annabi ya rasu
Har ila yau, mun kawo muku labarin cewa mai kula da kabarin Manzon Allah (SAW), Abdou Ali Idris ya riga mu gidan gaskiya a birnin Madinah.
Sheikh Abdou Ali kafin rasuwarsa shi ne ke kula da dakin Manzon Allah (SAW) wanda ya dade ya na hidima ga masallacin Madina.
Hukumar masallacin Harami sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a ranar Litinin 20 ga watan Nuwambar 2023 a birnin Madina.
Wata Hajiya daga Najeriya ta rasu
A wani labarin, kun ji cewa wata Hajiya daga jihar Lagos, Ramota Bankole ta riga mu gidan gaskiya yayin aikin hajji.
Ramota ta kasance jigon jam'iyyar APC a jihar wacce ta rike mukamin sakatariyar jin dadi ta jam'iyyar na tsawon lokaci.
Asali: Legit.ng