Yanzu-yanzu: Kungiyar Hezbollah na baiwa yan Shi’an Najeriya horo – Rahoton MEI

Yanzu-yanzu: Kungiyar Hezbollah na baiwa yan Shi’an Najeriya horo – Rahoton MEI

Majiya mai karfi da ke kusa da kungiyar Hezbollah ta bayyana cewa kungiyar da ke kasar Lebanon a yanzu hakatana baiwa yan Shi’an Najeriya horon soji a cikin kasar Lebanon, game da cewar rahoton da ma’aikatar yankin gabas ta tsakiya ta wallafa yau Alhamis.

Majiyar tace: “Dogayen mutane, sanye da riguna irin na Arewacin Najeriya, akan gansu a garin Dahieh, wani unguwar yan Shi’a da ke birnin Beirut inda Hezbollah ke da karfi.”

“Da farko mutanen da akewa wannan horo basu da yawa amma yanzu suna kara yawa. Da karatu kawai ake koya musu amma yanzu an fara horar da su Kaman soji a wurare biyu da ke garin Bekaa,”

Wannan abu bai bada mamaki ba yayinda rahotannin suka nuna cewa kasar Iran na taimakawa shugaban kungiyar da agajin kudi kuma suna kawo masa ziyara.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta hana raba wa talakawa kudin Abacha

Shugaban kungiyar Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, dan gain Zariya ne wanda ya fara gwagwarmayarsa a kungiyar yan uwa Musulmi. Amma daga baya ya koma kungiyar Shi’a inda ya zama wakili kasar Iran a Najeriya.

A shekarar 2015, jami’an sojin Najeriya sun hallaka akalla yan Shi’a 300 kuma sun damke shugabansu sanadiyar fito-na-fito da sukayi da babban hafsan sojin Najeriya, Tukur Buratai, a watan Disamban shekarar.

Har ila yau dai yana hannun hukuma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel