Bayan Kama Donald Trump da Laifuffuka, Shin Zai Iya Takarar Shugaban Kasar Amurka?

Bayan Kama Donald Trump da Laifuffuka, Shin Zai Iya Takarar Shugaban Kasar Amurka?

Wata kotu dake zamanta a Manhattan dake Amurka ta kama tsohon shugaban kasar, Donald Trump da manya-manyan laifuffuku 34, wanda ya sanya shi zama shugaban kasar na farko da za a yankewa hukunci kan aikata mugun laifi.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

America - Mafi akasarin laifukan da aka kama Mista Donald Trump da su sun danganci aikata rashin gaskiya a kasuwancinsa, tare da bayar da kudin tsohiyar baki don boye alakarsa da wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels, kamar yadda BBC ta wallafa.

Bayan tabbatar masa da laifukan, abin da zai fara yanzu ya rage shi ne jin anya Donald Trump zai iya sake tsayawa takarar shugaban kasar Amurka?

Kara karanta wannan

'Daɗi zai biyo baya' Masana sun fadi dalilin goyon bayan tsare tsaren Tinubu

Donald Trump
Duk da kama shi da mugayen laifuka, Donald Trump zai iya takarar shugaban Amurka Hoto: Win McNamee
Asali: Getty Images

Mabanbantan bayanai sun bayyana cewa wanda aka taba kamawa da laifi zai iya tsayawa takara a kasar idan ya cika wasu sharudda;

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai laifi zai iya tsayawa takarar Amurka?

Kila wannan ce tambayar da a yanzu duk mai bibiyar siyasar duniya tunani a ransa. A wani bayani da CNN Politics ta yi, amsa mafi gajarta da sauki ita ce 'Eh, kwarai'.

Kundin tsarin mulkin kasar Amurka ya gindaya sharudda guda uku da sai mutum ya cika su zai iya tsayawa takara.

Sharuddan su ne;

1. Mutum ya kasance dan kasa da aka haifa a kasar

2. Mutum ya kai akalla shekara 35 da haihuwa

3. Mutum ya zauna a kasar Amurka na akalla shekara 14

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya cika dukkanin wadannan sharudda.

Menene matsayin haramta takarar mai laifi

Kara karanta wannan

Maganar Firaministan Birtaniya mai kama da ta Pantami ta tayar da kura a Intanet

A wani gyara na 14 a kundin tsarin mulkin Amurka an bayyana cewa babu wani wanda ya taba mukamin gwamnati, kuma ya aikata laifi da zai sake zama wakilin kasar.

Amma tuni kotun kolin kasar ta zartar da hukunci kan kudurin, inda ta bayyana cewa dole sai majalisar Amurka ta zartar da doka ta musamman na tabbatar da haramcin.

Rahotanni na kuma nuna cewa wannan ba abu ne da za a yi kwana kusa ba. Ke nan Trump zai iya tsayawa takara duk da kudurin.

Amurka: Za a iya tura Trump gidan yari?

Jawabai da dama na ganin akwai yiwuwar Donald Trump ba zai yi zaman gidan yari ba duba da cewa wannan ne karo na farko da aka kama shi da aikata laifi.

Sai dai girman laifukan guda 34 da aka kama shi da su kuma ka iya kai ga a yanke masa zaman gidan kaso na wani lokaci.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

Sai dai Elie Honig, kwararre kan sharhi a harkokin shari'a na ganin kotun za ta iya yanke masa hukuncin tara da daurin talala.

An haramtawa 'yan Najeriya shiga Amurka

A baya mun baku labarin cewa mahukuntan kasar Amurka sun takawa wasu rukuni na 'yan Najeriya birki daga shiga kasarsu.

Gwamnatin Joe Biden ta bayyana cewa za ta hana duk wanda ke da hannun wajen magudin zabe a Najeriya takardar izinin shiga kasarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.