Iran: "Ka Mutu da Jinin Al'umma a Kanka", Amurka Ta Bijiro da Zargi Kan Marigayi Raisi
- Duk da mika sakon ta'aziyya a hukumance, kasar Amurka ta zargi marigayi shugaba Ebrahim Raisi na Iran da ta'addanci
- Amurka ta nuna damuwa kan yadda marigayin ya bar duniya da alhakin mutane da dama musamman a yankin Gabas ta Tsakiya
- Kasar Amurkar ta zargi Raisi da goyon bayan kungiyayon ta'adanci a yankin wanda suka yi ajalin mutane da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Washington, Amurka - Kasar Amurka ta zargi marigayi shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi da ta'addanci.
Amurka na zargin Ebrahim Raisi da goyon bayan kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin addini a yanki Gabas ta Tsakiya.
Raisi: Amurka ta tura sakon jaje Iran
Wannan na zuwa ne bayan kasar ta tura sakon ta'aziyya a hukumance ga Iran kan rasuwar shugabanta, cewar UK independent.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kirby ya ce babu tantama Raisi mutum ne wanda ya goyi bayan ta'addanci a yankin Gabas ta Tsakiya wurin marawa wasu kungiyoyi baya.
Kakakin tsaron kasar a 'White House', John Kirby ya bayyana a haka yayin wata ganawa da manema labarai, Channels TV ta tattaro.
Iran: Amurka ta zargi Raisi da ta'addanci
"Babu wata tababa, wannan mutum ne wanda ya dauki alhakin kisan mutane da dama kuma yana dauke da jininsu a hannunsa."
- John Kirby
Kirby ya ce gwamnatin Amurka za ta ci gaba da zargin Iran da laifin lalata lamuran yankin Gabas ta Tsakiya.
Ta'aziyyar Amurka ga mutanen Iran
Har ila yau, mai magana da yawun gwamnatin, Matthew Miller ya mika da ta'aziyya a hukumance kan mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi.
Da aka tambaye shi kan martanin kasar kan mutuwar, Miller ya ce Amurka ta yi irin wannan martani ga shugabanni da suka mutu wanda ake zargi kamar Josef Stalin.
Miller ya ce Amurka ba za ta goyi bayan duk wani yunkuri na take hakkin dan Adam ba.
Shugaban Iran, Ebrahim Raisi ya rasu
A wani labarin, an ji shugaban ƙasar Iran, Ebrahim Raisi, ya rasa ransa a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ranar Lahadi 19 ga watan Mayu.
Hatsarin jirgin wanda ya rutsa da wasu jami'an gwamnatin ƙasar ya yi sanadiyyar rasuwar dukkanin mutanen da ke cikin jirgin mai saukar ungulu.
Jami'ai ne suka tabbatar da rasuwar Ebrahim Raisi da sauran mutanen da hatsarin ya ritsa da su a safiyar ranar Litinin 20 ga watan Mayu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng