Jerin Shugabannin Kasashe 15 da Suka Rasu a Hatsarin Jirgin Sama
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Shugaban ƙasar Iran, Ebrahim Raisi ya gamu da.ajalinsa a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayun 2024.
Ebrahim Raisi ya zama shugaban ƙasa na 15 wanda ya rasa ransa sakamakon hatsarin jirgin sama a tarihi tun daga shekarar 1940.
Shugabannin da suka rasu a hatsarin jirgin sama
Jaridar Gazettengr ta jero shugabannin ƙasashe 15 da suka rasu a hatsarin jirgin sama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. José Félix Estigarribia
Shugaban ƙasar Paraguay na 34, José Félix Estigarribia ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ranar 7 ga watan Satumba, 1940 a Altos, Paraguay. Ya mutu a cikin jirgin Potez 25.
2. Ramon Magsaysay
Ramon Magsaysay shugaban ƙasar Philippines na bakwai, ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ranar 17 ga watanMaris, 1957, a Dutsen Balamban, Cebu.
Ya gamu da ajalinsa a cikin jirgin Douglas C-47 Skytrain.
3. Nereu Ramos
Nereu Ramos wanda ya zama shugaban riƙon ƙwarya na Brazil bayan Shugaba Getúlio Vargas ya mutu ta hanyar kashe kansa, ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ranar 16 ga watan Yuni, 1958.
Nereu ya mutu ne a cikin jirgin Douglas C-47 Sktrain a kusa da filin jirgin saman Curitiba Afonso Pena.
4. Abdul Salam Arif
Abdul Salam Arif shugaban ƙasar Iraki na biyu, ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ranar 13 ga watan Afrilu, 1966, a birnin Baghdad.
Ya mutu a cikin jirgin Havilland Dove.
5. Castelo Branco
Castelo Branco ya zama shugaban mulkin soja na farko a ƙasar Brazil bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 1964.
Ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ranar 18 ga watan Yuli, 1967, a Fortaleza, Brazil, a cikin jirgin Piper PA-23.
6. René Barrientos
Shugaban ƙasar Bolivia na 47, ya mutu a cikin jirgin sama a ranar 27 ga watan Afrilu, 1969, a Arque, Bolivia, a cikin jirgin Hughes 369.
7. Jaime Roldos Aguilera
Shugaban ƙasar Ecuador ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ranar 24 ga watan Mayu, 1981, a Dutsen Huairapungo, Celica Canton na Lardin Loja, Ecuador.
Ya mutu ne tare da ministan tsaronsa, mataimakansa da matansu a cikin wani jirgin saman Avro 748.
8. Samora Machel
Shugaban ƙasar Mozambique na farko daga samun ƴancin kai a shekarar 1975, ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ranar 19 ga watan Oktoba, 1986, a Mbuzini, na ƙasar Afrika ta Kudu, a cikin jirgin Tupolev Tu-134.
9. Muhammad Zia-ul-Haq
Shugaban ƙasar Pakistan na shida ya mutu a cikin jirgin sama a ranar 17 ga watan Agusta, 1988 a Bahawalpur, Pakistan. Ya mutu a cikin jirgin Lockheed C-130 Hercules.
10. Juvénal Habyarimana
Shugaban ƙasar Rwanda na biyu, an harbo jirginsa na Dassault Falcon 50 kusa da filin jirgin sama na Kigali a ranar 6 ga watan Afrilu, 1994.
11. Cyprien Ntaryamira
Shugaban ƙasar Burundi, ya mutu bayan shafe watanni biyu yana mulki tare da Habyarimana na Rwanda a cikin jirgin Dassault Falcon 50 da aka harbo a kusa da filin jirgin sama na Kigali a ranar 6 ga Afrilu, 1994.
12. Boris Trajkovski
Boris Trajkovski ya shugabanci North Macedonia daga 1999 har ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ranar 26 ga Fabrairu, 2004, a Mostar, Bosnia and Herzegovina, a cikin wani jirgin saman Beechcraft Super King Air.
13. Lech Kaczyński
Lech Kaczyński ya shugabanci ƙasar Poland daga 2005 har ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a Smolensk, Russia a ranar 10 ga watan Afrilu, 2010.
Ya mutu tare da matarsa, Maria Kaczyńska, da wasu manyan jami'an soji da mataimaka a cikin wani jirgin Tupolev Tu-154.
14. Sebastián Piñera
Shugaban ƙasar Chile daga 2010 zuwa 2022, ya mutu a wani jirgin sama mai saukar ungulu na Robinson R44 mintuna kaɗan bayan tashinsa a tafkin Ranco, Chile, a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2024.
15. Ebrahim Raisi
Ebrahim Raisi shugaban ƙasar Iran na takwas, ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ranar 19 ga watan Mayu, 2024, a Varzaqan, Gabashin Azerbaijan, Iran, a cikin wani jirgi mai saukar ungulu ƙirar Bell 212, cewar rahoton The Guardian.
Wanda zai gaji Ebrahim Raisi
A wani labarin kuma, kun ji cewa an fara maganar wanda zai zama sabon shugaban ƙasar Iran biyo bayan mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi.
Alamu sun nuna cewa mataimakin shugaban kasar Iran, Muhammad Mokhber ne ake tsammani zai rike shugabancin ƙasar wacce ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng