Abin da Muka Sani Game da Hatsarin Jirgin Sama da Ya Kashe Shugaban Iran

Abin da Muka Sani Game da Hatsarin Jirgin Sama da Ya Kashe Shugaban Iran

Hadarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya kashe shugaban kasar Iran da ministan harkokin wajen kasar ya jefa jimami a Iran da duniya baki daya.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An ruwaito cewa an gano gawarwakin shugaban kasar Ebrahim Raisi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, da sauran su a yau Litinin.

Wannan na zuwa ne bayan shafe sa'o'i ana bincike a cikin wani daji mai tsaunuka da ke Arewa maso Yammacin kasar, in ji rahoton IRNA, kafar yada labaran Iran.

Abin da muka sani game da mutuwar shugaban Iran, Ebrahim Raisi
Hatsarin jirgin sama ya kashe shugaban IRan, abin da muka sani zuwa yanzu. Hoto: @raisi_com
Asali: Twitter

Ga abin da muka sani daga Iran:

Mutanen jirgin da inda suka dosa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ana jimamin mutuwar shugaban kasar Iran, an kwantar da sarkin Saudiya a asibiti

Jirgin na dauke da Raisi, Amir Abdollahian, gwamnan lardin gabashin Azarbaijan na Iran da sauran jami'ai a lokacin da ya yi hatsari, kamar yadda kamfanin labarai na AP ya ruwaito.

Raisi yana dawowa ne a ranar Lahadi bayan zuwa iyakar Iran da Azarbaijan domin kaddamar da wani madatsar ruwa tare da shugaban Azarbaijan Ilham Aliyev lokacin da hadarin ya faru.

IRNA ta ce hatsarin ya hallaka mutane takwas, ciki har da ma'aikatan jirgin uku da ke cikin jirgin kirar Bell, wanda Iran ta saya a farkon shekarun 2000.

Gudanar da aikin ceto a kasar Iran

Jami'an Iran sun ce sarkakiyar tsaunuka, dazuzzuka da kuma hazo ne suka kawo tsaiko ayyukan ceto da aka fara a ranar Lahadi.

Shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran, Pir-Hossein Koulivand, ya ce kungiyoyin bincike 40 ne aka girke a kasa duk da "kalubalen yanayi."

Saboda mummunan yanayi na hazo, "ba a iya gudanar da bincike da jirage marasa matuka ba, in ji Koulivand, a cewar IRNA.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da shugaban kasar Iran ya samu matsala, ya yi muguwar saukar gaggawa

Yadda aka gano inda jirgin ya fadi

Da sanyin safiyar litinin, hukumomin Turkiyya suka fitar da wani hoto da ke nuna wani abu kamar gobara a cikin jeji da ake kyautata zaton a nan ne jirgin ya fadi.

Lambobin taswirar da ke jikin hoton sun nuna gobarar jirgin a tazarar kilomita 20 daga Kudu da iyakar Azarbaijan da Iran a gefen wani tsauni mai tsayi.

Hotunan da kafar IRNA ta fitar sun nuna abin da hukumar ta bayyana a matsayin wurin da hatsarin ya afku, yayin da daga bisani aka tabbatar da cewa babu wanda ya tsira daga hatsarin.

Yadda mutuwar Raisi za ta shafi Iran

Ana kallon Raisi a matsayin majibincin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei kuma mai yuwuwa wanda zai maye gurbinsa a cikin tsarin mulkin Shi'a na kasar.

A karkashin kundin tsarin mulkin Iran, idan shugaban kasa ya mutu, mataimakin shugaban kasar na farko (a wannan yanayin, Mohammad Mokhber) zai zama shugaban kasa, ji rahoton IRNA.

Kara karanta wannan

CNG: Manyan matakai 3 da Tinubu ya dauka na janye Najeriya daga dogara da man fetur

Khamenei ya tabbatar wa Iraniyawa a bainar jama'a cewa "ba za a samu cikas ga ayyukan kasar ba" sakamakon hatsarin jirgin.

Abin da kasashen duniya ke cewa

Bayan da labarin ya fara bayyana na aikin ceto, kasashe da suka hada da Rasha, Iraki da Qatar sun yi bayani a hukumance na nuna damuwa game da makomar Raisi.

Saudiya, wacce a al'adance abokiyar gaba ce da Iran, duk da cewa kasashen biyu sun yi sulhu a baya-bayan nan, ta ce tana tare da Iran a cikin wannan mawuyacin hali.

Shugaban Azarbaijan Aliyev ya ce zai ba da duk wani tallafi da ya dace. Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kasance cikin dari-dari saboda alakar diflomasiyyar Azarbaijan da Isra'ila, babbar makiya yankin Iran.

An kwantar da Sarki Salman a asibiti

A wani labarin, mun ruwaito cewa an kwantar da Sarki Salman na Saudiya a asibitin fadar Al Salam da ke a Jeddah a kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

A karon farko, an yi bikin nuna ado a Saudiyya da mata suka fitar da cinyoyinsu waje

A wani gwaji da aka yiwa basaraken, an gano cewa ya kamu da cutar huhu, dalilin da ya sa aka kwantar da shi domin yi masa magani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel