Ana Jimamin Mutuwar Shugaban Kasar Iran, an Kwantar da Sarkin Saudiya a Asibiti

Ana Jimamin Mutuwar Shugaban Kasar Iran, an Kwantar da Sarkin Saudiya a Asibiti

  • An kwantar da sarkin Saudiya, Salman bin Abdulaziz a asibiti bayan da gwaji ya tabbatar da cewa yana fama da cutar huhu
  • An ruwaito cewa za a yiwa sarkin mai shekaru 88 magani a fadar Al Salam da ke birnin Jeddah har sai kumburin huhun ya lafa
  • Wannan na zuwa ne yayin da duniya ke jimamin mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi a wani hatsarin jirgin sama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A yayin da duniya ke jimamin mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi, a hannu daya kuma, an kwantar da sarkin Saudiya, Salman bin Abdulaziz a asibiti.

An kwantar da sarkin Saudiya a asibiti
Ana jimamin mutuwar shugaban kasar Iran, an kwantar da sarkin Saudiyya Salman a asibiti. Hoto: @raisi_com, @KingSalman
Asali: Twitter

Saudiya: Salman ya kamu da cutar huhu

A ranar Lahadi ne aka ruwaito sarkin Saudiyya Salman zai yi jinya a fadar Al Salam da ke birnin Jeddah, bayan da aka yi masa gwajin cutar huhu.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafar labaran Reuters ta ruwaito shafin sadarwa na yanar gizo na fadar gwamnatin kasar na cewa, za a yiwa sarkin mai shekaru 88 magani har sai kumburin huhun ya lafa.

Tun da fari, kamfanin dillancin labaran Saudiya ya bayyana cewa, an yi wa Sarki Salman gwajin lafiya a asibitocin masarautar da ke fadar Al Salam sakamakon “zafin jiki da ciwon gabobi”.

Yariman Saudiya ya dage ziyarar Japan

Sakamakon rashin lafiyar Sarki Salman, yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, shugaban Saudiyya, ya dage ziyarar da zai kai Japan.

Babban sakataren majalisar ministocin kasar Japan Yoshimasa Hayashi ya bayyana dage ziyarar da Yarima Mohammed ya shirya kai wa yau Litinin.

Shugaban Iran, Ebrahim Raisi ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya mutu bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu da ya ke dauke da shi da wasu jami'ai ya yi hadari.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da shugaban kasar Iran ya samu matsala, ya yi muguwar saukar gaggawa

Masu aikin ceto sun gano jirgin da ke dauke da shugaban kasar da kuma ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian bayan da ya fado a yankin Arewa maso yammacin Iran.

Ebrahim Raisi, mai shekaru 63, wanda ke wakiltar bangarorin da ke da tsatsauran ra'ayi a siyasar Iran, ya shafe kusan shekaru uku yana shugabancin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.