Kasar Turkiyya Ta Gimtse Alakar Kasuwanci da Isra’ila Saboda Gallazawa Falasdinawa
- Shugaban kasar Turkiyya, Recep Erdogan, ya dauki matakin dakatar da harkokin kasuwanci tsakanin sa da Isra'ila
- Ma'aikatar kasuwanci ta kasar ta ce sun dauki matakin ne domin lura da yadda Isra'ila ke musgunawa Falasɗinawa
- Ministan harkokin wajen Isra'ila, Israel Katzsaid ya yi Allah wadai da matakin tare da bayyana abin da suka yi domin samun mafita
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Erdogan, ya sanar da dakatar da harkokin kasuwanci da kasar Isra'ila.
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar ta ce daukan matakin yana da alaka da musgunawa Falasɗinawa da Isra'ila ke yi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kasuwanci da Turkiyya ta dakatar ya shafi dukkan nau'o'in cinikayya da kayayyaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasar Turkiyya dama ta kasance cikin jerin ƙasashen da suke nuna wa Isra'ila yatsa tun fara kai hare-haren da ta yi zuwa Gaza a watan Oktoban shekarar 2023.
Sharadin dawo da alakar Turkiyya-Israila
Ma'aikatar kasuwancin ta ce matakin shine daidai a halin yanzu amma ta bada sharadi daya domin janye shi.
Ta shardanta cewa gimtse alakar kasuwancin za ta cigaba har sai Isra'ila ta bude kofa wurin shigar da kayan agaji zuwa Gaza, cewar jaridar the Gurdian
Kasashen biyu sun dade suna kulla alakar kasuwanci tsakaninsu wanda a shekarar 2023 kawai sun yi kasuwanci da ya kai na dala biliyan 6.8
Martanin kasar Isra'ila ga Turkiyya
A ranar Alhamis da ta wuce ne ministan harkokin wajen Isra'ila, Israel Katzsaid ya yi martani ga matakin da Turkiyya ta dauka.
Mista Katzsaid ya ce lalle kasar Turkiyya ta karya yarjejeniyar kasuwancin kasa da kasa kuma dama haka 'yan kama karya suke.
Sannan ya ce ya umurci ma'aikatar harkokin wajen kasar da su samar da wasu hanyoyin da za su cigaba da samar da kayayyaki ga mutanen su.
An kashe mutane 13,000 a Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa akalla mutane 13,000 ne suka mutu sakamakon farmakin da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kan mazauna zirin Gaza tun watan Oktoba.
Yakin ya barke ne tsakanin dakarun Hamas da kuma sojojin Isra'ila kan farmakin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.
Asali: Legit.ng