Kungiyar Tarayyar Turai Ta Kakabawa Iran Sabon Takunkumi Kan Harin da Ta Kai Isra’ila
- Kungiyar tarayyar turai (EU) ta sanar da sabon takunkumi da ta kakabawa Iran a matsayin horo kan harin da ta kai a Isra'ila
- Shugabannin kungiyar sun dauki matakin ne bayan wani taron gaggawa da suka yi a birnin Brussels bayan fara rikicin Iran da Isra'ila
- Shugaban kungiyar, Charles Michael ya ce dole ne su cigaba da mayar da Iran saniyar ware a cikin dukkan al'amura har sai ta dawo cikin hankalinta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta amince da sanyawa kasar Iran takunkumi biyo bayan harin ramuwar gayya da ta kai Isra'ila.
Shugabannin sun amince da sabon takunkumin ne a wani taro da suka gabatar a birnin Brussels domin daukan mataki a kan harin da Iran ta kai wa Isra'ila ranar Asabar.
Abin da takunkumin Iran zai shafa
Sabon takunkumin zai shafi kere-keren da Iran ke yi ne na jirage marasa matuka da makamai masu linzami wanda da su ta kai hari zuwa Isra'ila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa sabon takunkumin ya zo ne bayan takunkumin hana Iran sayar da jirage marasa matuka wa tarayyar Rasha tun bayan fara yakinta da Ukraniya.
Isra'ila ta bukaci sa wa Iran takunkumi
Tin bayan da Iran ta kai harin ramakon dai Isra'ila ta rinka kira ga kawayenta domin daukan mataki a kan Iran, cewar jaridar Al-Jazeera.
A wurin taron, shugaban kungiyar tarayyar Turai, Charles Michael, ya tabbatar da cewa dole ne su mayar da Iran saniyar ware saboda abinda ta aikata, cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Tun bayan harin ramakon da Iran ta kai ranar Asabar, har yanzu Isra'ila ba ta dauki matakin soji domin mayar da martanin ba.
Saudiyya ta musanta tallafawa Isra'ila
A wani rahoto kuma, kun ji cewa kasar Saudiyya ta musanta tallafawa Isra'ila wurin kakkabo jiragen yakin da Iran ta harba mata ranar Asabar data wuce.
Kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar ne biyo bayan jita-jita da ake yadawa a kan tana cikin kasashen da suka tallafawa Isra'ila a lokacin harin.
Asali: Legit.ng