Ruwan sama ya yi awon gaba da gonaki 3000 da gidaje 120 a Jigawa

Ruwan sama ya yi awon gaba da gonaki 3000 da gidaje 120 a Jigawa

- Mamakon ruwan sama ya jawo ambaliya a garin Zugo da ke karamar hukumar Guri a jihar Jigawa

- Ambaliyar ta yi awon gaba da gidaje 120 da kuma gonaki 3,000

- Tuni dai gwamnatin karamar hukumar ta yi taimakon gaggawa ta hanyar tura matasa sama da 150 da buhunan yashi sama da 1,000 don daure bakin kogin Guri

Mamakon ruwan sama wanda ya jawo ambaliyar ruwa, ya yi awon gaba da gidaje 120 da gonaki 3,000 at garin Zugo da ke karamar hukumar Guri a jihar Jigawa.

A ranar Alhamis ne jami'in yada labarai na yankin, Sanusi Doro, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labarai, NAN aukuwar abin a sa'o'in karshe na ranar Talata.

KU KARANTA: Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa

Ya ce ambaliyar ruwan ta wanke titin Una-Zugobia, abinda ya hana mutane da mafanin gona isa kasuwa a ranar.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da hukumar agajin gaggawa ta jihar da su gagauta taimakawa jam'ar da abin ya faru dasu da magunguna da kuma kayan abinci.

Hakazalika, Doro ya ce karamar hukumar ta sanya matasa su zuba buhunan yashi a gabar kogin Guri don daure gabar gudun cigaban ambaliyar.

"Karamar hukumar ta gaggauta kai dauki ta hanyar tura matasa sama da 150 da buhunan yashi sama da 1,000 don daure gabar kogin Guri, gudun cigaban ambaliyar."

"An yi hakan ne don gudun cigaban ambaliyar ruwan saboda mutane da yawa sunyi asarar amfanin gona da suka hada da masara, dawa, gero da sauransu." inji jami'in

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel