Jerin jihohin da ambaliyar ruwa zai shafa a wannan shekarar

Jerin jihohin da ambaliyar ruwa zai shafa a wannan shekarar

A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar dukiyoyi harma da rayuka a wasu jihohi na fadin kasar nan. Sai dai a wannan shekarar gwamnatin tarayya ta bayar da hasashen yadda za ta magance matsalar

Ya zama wajibi ga gwamnati ta sanar da mutane halin da ake ciki akan ambaliyar ruwa a kowacce shekara. Hasashen da gwamnatin za ta bayar zai taimaka mutuka ga 'yan Najeriya da wasu jihohi da ke zaune a wuraren da ambaliyar za ta faru, domin su tashi tsaye wurin neman mafita.

Najeriya ta na samun ruwa mai yawa daga kasashen da suke makwabtaka da ita kusan guda bakwai, wanda duka ruwan su yake wucewa ta cikin Najeriya.

Sai dai kuma, duk da fadakarwar da gwamnatin ta ke yi akan ambaliyar, duk shekara sai an samu asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa a fadin kasar. Hakan kuma na faruwa ne saboda rashin daukar sanarwar da gwamnatin ta ke da muhimmanci ga mutane.

Jerin jihohin da ambaliyar ruwa zai shafa a wannan shekarar
Jerin jihohin da ambaliyar ruwa zai shafa a wannan shekarar
Asali: Facebook

Misali, a shekarar 2018, kimanin mutane 441,251 abin ya shafa, cikin kananan hukumomi 50, a cewar hukumar taimakon gaggawa ta kasa.

A wannan shekarar m hukumar ta bayar da sanarwar ga jihohi da ma 'yan Najeriya baki daya, inda ta bayyana cewa akwai yiwuwar samun ambaliya ga kananan hukumomi 600 a fadin kasar nan, idan damina ta tsaya da kyau.

Kananan hukumomin da abin zai shafa sun hada da: Katsina – Musawa; Kebbi – Dandi, Kalgo, Koko/Besse, Suru, Aliero, Argungu, Augie, Bagudo, Birnin–Kebbi, Bunza, Ngaski, Shanga; Niger – Borgu, Agwara, Magama, Lapai, Mokwa, Shiroro, Wushishi, Bida, Edati, Gbako, Mashegu, Munya; Sokoto – Sabon Birni, Tambuwal, Wurno,Yabo, Gwadabawa, Goronyo, Isa, Kware, Rabah, Shagari Bodinga, Tureta, Silame, Dange–Shuni, Wurno, Yabo, Wamako; Zamfara – Maru, Talata-Mafara, Zurmi, Birnin-Magaji/ Kiyawa, Bakura, Bungudu Shinkafi, Gusau, Kaura–Namoda, Maradun; Kaduna- Kauru, Soba, Chikun, Igabi, Kaduna South.

Sannan akwai kananan hukumomin: Kwara – Asa, Ilorin West, Oyun, Pategi; Adamawa – Demsa, Fufore, Gombi, Numan, Shelleng, Yola North, Yola South; Gombe – Balanga, Dukku, Funakaye, Gombe, Kwami, Nafada; Taraba – Ardo-Kola, Karim Lamido, Jalingo, Lau, Ibi; Nasarawa – Keffi, Nassarawa–Eggon, Keana, Doma, Toto, Nassarawa; Benue – Tarka, Buruku, Guma, Agatu, Tarka; Delta – Aniocha North, Bomadi, Ndokwa East, Ndokwa West, Oshimili North, Oshimili South, Patani, Ughelli South; Rivers – Abua/Odual, Ahoada East, Ahoada West, Akuku-Toru, Andoni, Asari-Toru, Bonny, Gokana, Ogu/Bolo, Okrika, Opobo/Nkoro, Port-Harcourt; Anambra – Anaocha, Awka South, Dunukofia, Njikoka, Ogbaru, Orumba North, Oyi; Imo – Aboh-Mbaise, Ezinihite, Ideato South, Ideato North, Ihitte/Uboma, Isiala Mbaitoli, Isu, Mbaitoli, Nkwerre, Obowo, Okigwe, Orlu, Owerri Municipal, Owerri North, Owerri West, Unuimo; Cross River – Akpabuyo, Bakasi, Biase, Calabar, Ikom, Obubra, da kuma Yalla.

KU KARANTA: Ashe jami'an 'yan sandan dake jihar Lagos kasuwanci suke zuwa yi ba aiki ba

An bayar da sanarwar cewa jihohi 36 dake fadin kasar nan za su samu ambaliyar a cikin yanayi daban-daban.

A cikin sanarwar da ministan ruwa, Suleiman Adamu ya fitar a ranar Talata, yayi gargadin cewa ambaliyar ruwan za ta faru ne sanadiyyar yawan ruwan sama da za a samu a wannan shekarar, ko kuma sanadiyyar sakin ruwa da wasu kasashe da suke makwabtaka da kasar nan za su yi.

Ya bayyana jihohin da abin zai shafa, wadanda suka hada da: Lagos, Rivers, Benin, Benue, Kaduna, Sokoto, Ibadan, Niger, Anambra, Imo, Cross River, Delta, Yobe, Ogun, Osun, Bayelsa, Rivers, Ondo, Adamawa, Borno, Jigawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel