IMF Ta Yi Hasashen Saukar Farashin Kayayyaki a Najeriya Cikin Shekarar 2025
- A wani sabon bahasi, asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya yi hasashen saukar farashin kayayyaki a tarayyar Najeriya cikin shekarar 2025
- Ya kuma kara da hasashen haɓakar tattalin arzikin kasar cikin wannar shekarar lura da cigaba da ake samu a harakar noma da tsaro
- Shugaban sashen bincike na IMF, Daniel Leigh, ne ya bayyana hasashen ya kuma yi kira ga Najeriya da ta cigaba da ɗaukan matakan da suka kamata domin haɓaka tattalin arziki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
A cikin sanarwar da ya fitar na hasashen tattalin arziki, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa.
Tabbatar hasashen na nuna cewa za a samu gagarumin sauyi na hauhawar farashin kayayyaki a fadin ƙasar.
Shugaban sashen bincike na IMF, Daniel Leigh, ya bayyana tasirin da sauye-sauyen tattalin arzikin zai kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar jaridar the Punch, sauye-sauyen da ake hasashe sun hada da daidaita farashin musaya, wanda ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki zuwa kashi 33.2 cikin dari a watan Maris.
Tashin farashin kaya a Najeriya
A cewar hasashen yawan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 33.2% bisa ga bayanan baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar.
Hakanan hauhawar farashin abinci ya karu zuwa sama da kashi 40% a farkon shekarar 2024
Yadda saukar farashin zai kasance
A cewar jaridar Channels Television, Leigh ya ce hasashen su ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki zai ragu zuwa kashi 23 cikin dari a shekara mai zuwa sannan kashi 18 zai ragu cikin shekarar 2026.
Ya kuma yi karin haske kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya da ake sa ran zai tashi daga kashi 2.9 a bara zuwa kashi 3.3 cikin 100 a bana.
Ya kuma danganta hakan ne sakamakon farfadowar da ake samu a fannin man fetur, da inganta tsaro, da kuma ci gaba a fannin noma.
Hauhawar farashi zai kawo talauci a Najeriya
A wani rahoton kuma, kun ji cewa, Babban Bankin Duniya (WB) ya yi hasashen cewa akalla 'yan Najeriya miliyan 2.8 ne za su shiga kangin talauci nan da karshen shekarar 2023 zuwa 2024.
Bankin ya ce za a samu karuwar wadanda za su talauce ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kuma karancin habakar tattalin arzikin Najeriya.
Asali: Legit.ng