"Abin Takaici Ne", Shehu Sani Ya Magantu Game da Harin da Iran Ta Kai Kan Isra'ila
- Yayin da Iran ta kai harin ramuwar gayya kan Isra'ila, Sanata Shehu Sani ya yi martani kan lamarin
- Sanatan ya ce shugabannin duniya sun ji kunya ganin yadda Gabas ta Tsakiya ke neman fadawa cikin mummunan yaƙi
- Wannan na zuwa ne bayan Iran ta kai harin ramuwar gayya kan Isra'ila a jiya Asabar 13 ga watan Afrilu a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi martani kan harin Iran a Isra'ila.
Sanatan ya ce wannan abin kunya ne kuma shugabannin duniya sun gaza a wannan karon.
Shehu Sani ya kalubalanci shugabannin duniya
Shehu Sani ya bayyana haka a shafinsa na X a daren jiya Asabar 13 ga watan Afrilu yayin da Iran ta kai hari a Isra'ila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan abin kunya ne a kai hari yayin da shugabannin duniya ke neman yadda za a sulhunta lamari.
"Isra'ila ta kai hari kan ofishin jakadancin Iran a Syria, sannan Iran ta kai harin ramuwar gayya kan kasar Isra'ila."
"A gaban idonmu, Gabas ta Tsakiya za ta tsunduma cikin yaki, duk matakan da majalisar Ɗinkin Duniya ta dauka an yi fatali da su, shugabannin duniya sun gaza."
- Shehu Sani
Musabbabin kai harin Iran kan Isra'ila
Wannan martani na Sanatan na zuwa ne bayan Iran ta kai mummunan hari kan Isra'ila a jiya Asabar 13 ga watan Afrilu.
Hakan ya biyo bayan harin da Isra'ila ta kai a ofishin jakadancin Iran da ke kasar Syria a kwanakin baya.
Harin da aka kai kan ofishin jakadancin Iran a Syria ya yi sanadin mutuwar manyan jami'an gwamnatin kasar.
Iran ta dauki matakin kai harin ramuwar gayyar inda ta bijirewa matakan da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da sauran kasashen duniya suka yi, cewar Aljazeera.
Sani ya magantu kan El-Rufai da Uba
A baya, kun ji labarin cewa Sanata Shehu Sani ya yi martani kan rikicin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da kuma Gwamna Uba Sani.
Sanatan ya ce tun farko ya taba ba El-Rufai shawara kan yawan cin bashi a jihar amma mutane suka yi ta cin mutuncinsa kan lamarin.
Asali: Legit.ng