So guba: Wani magidanci ya kwankwadi ruwan batir bayan ya kama matar sa da kwarto

So guba: Wani magidanci ya kwankwadi ruwan batir bayan ya kama matar sa da kwarto

Wani magidanci mai shekaru 40 a duniya mai suna Reggies Chiyanke a yanzu haka kamar yadda muka samu labari yana kwance a wata asibiti yana karbar kulawar likita bayan da ya kwankwadi ruwan batir lokacin da ya kama matar sa da kwarto.

Majiyar mu dai ta shaida mana cewa wannan shine karo na biyu da shi magidancin yana shan ruwan batir bayan kama matar sa da kwarton wanda kusan a iya cewa halin matar ne bin maza.

So guba: Wani magidanci ya kwankwadi ruwan batir bayan ya kama matar sa da kwarto
So guba: Wani magidanci ya kwankwadi ruwan batir bayan ya kama matar sa da kwarto
Asali: UGC

KU KARANTA: An kaso jirgin karyar fadar shugaban kasa Buhari

Legit.ng Hausa ta samu cewa jama'ar gari dai da dama sun shaidi matar ta Mista Chiyanike da cewa tana bin maza wanda kusan ma a iya cewa hakan ya zamar mata tamkar jiki.

A wani labarin kuma, Wani mutum magidanci mai shekaru akalla 35 a duniya mai suna Mista Achibong Patrick mun samu labarin cewa a ranar Laraba ya kashe dukkan 'ya'yan sa hudu kafin daga bisani shima ya kashe kan sa a gidan sa dake a kauyen Alesa, a karamar hukumar Eleme, jihar Ribas.

Kamar dai yadda muka samu daga wani da ganau, ya bayyana cewa magidancin Mista Patrick wanda dan asalin karamar hukumar Ogoja ne ta jihar Kuros Ribas sun samu sabani da matar sa kafin afkuwar lamarin inda har ma ta gudu ta bar shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng