Tirkashi: Wani mutumi ya watsa wa mutane 8 ruwan batir a kasuwar Anambra

Tirkashi: Wani mutumi ya watsa wa mutane 8 ruwan batir a kasuwar Anambra

Rahotanni sun kawo cewa an kai wa wasu mutane takwas hari da ruwan guba wato acid a kasuwar Ngbuka da ke Uguwagba, Awada kusa da Onitsha, jihar Anambra.

Wani mutumi da ya tsere ne ya far wa mutanen su takwas, inda ya zuba masu ruwan batir bayan sabani ya shiga tsakaninsa da wani mutum mai suna Onyeka.

“Yana zuba masu ruwan baitirin, sai ya tsere sannan mutane suka bi sahunsa da gudu amma ya tsere ma ganinsu," inji wani da abun ya faru a idonsa.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar, Haruna Mohammed, yace an kwashi mutaneen zuwa asibitin St. Martin, Ugwuagba domin samun kulawar likita.

“Wani matashi wanda ba a tabbatar da sunansa da adireshinsa ba ya samu sabani da wani mutum mai suna Onyeka Nwachukwu, mai shekara 38, a kasuwar Ngbuka da ke Ugwuagba, Awada.

“A cikin haka, sai mai laifin wanda a yanzu ya gudu ya kaima wasu mutane hari da ruwan batir,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Mutuwar ‘yar shugaban Yarbawa: Sai da na gargade ku kan Buhari – Fayose ga yan Najeriya

Ya bayyana sunayen wadanda lamarin ya cika dasu a matsayin Onyeka Nwachukwu (38), Ofili Benjamin (32) da kuma Ofili Damian (42).

Sauran sun hada da Okoro Ebuka (23), Ekwueme Anayo (35), Nnamani Chukwu (23), Obiora Chidubem(18) da kuma Obasi Solomon (24).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel