An Nemi Sunan Najeriya an Rasa a Jerin Kasashe 20 Mafi Farin Ciki a Duniya a 2024
An ayyana kasar Finland a matsayin ƙasar da ta fi ko ina farin ciki a fadin duniya, yayin da Najeriya ta gaza shiga jerin 20 ɗin farko na jadawalin kasashe mafi farin ciki a 2024.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rahoton kasashe mafi farin ciki na fitar da kididdigar sama da kasashe 140 da ke a fadin duniya, kuma an fara fitar da rahoton ne a shekarar 2012.
Kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa, ana fitar da jerin sunayen ne ta hanyar la'akari da ci gaban kasa, kudin shigar jama'a da kiwon lafiya.
Haka zalika ana duba ƴancin mutane a ƙasar, jin ƙansu da kuma ƙarfin yaki da talauci na kasashe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayani a kan mujallar 'Farin Ciki'
Rahoton mujallar 'Kasashe Mafi Farin Ciki' a duniya a 2024, ya nuna cewa Findland ce a gaba sai Denmark mai bi mata da kuma Iceland a na uku da Sweden a na hudu.
Kasar Norway a wannan karon ta zo na bakwai yayin da Birtaniya ta zama a ɓutar na jadawalin sahun 20 na farko a rahoton.
Talabijin na CNN ya ruwaito cewa John Helliwell, shi ne ya assasa mujallar kasashe mafi farin ciki a duniya.
Ya kasance farfesa ne a tattalin arziki wanda ke koyarwa a jami'ar British Columbia da kwalejin tattalin arziki ta Vancouver.
Jerin ƙasashe 20 da aka fi farin ciki
1. Finland
2. Denmark
3. Iceland
4. Sweden
5. Israila
6. Netherlands
7. Norway
8. Luxembourg
9. Switzerland
10. Australia
11. New Zealand
12. Costa Rica
13. Kuwait
14. Austria
15. Kanada
16. Belgium
17. Ireland
18. Czechia
19. Lithuania
20. Birtaniya
2024: Kasashen da ya kamata ku ziyarta
A wani rahoton kuma, Legit Hausa ta tattara bayani kan wasu ƙasashen duniya 5 da ya kamata ku ziyarta a 2024.
Masu yawon bude ido a fadin duniya na ci gaba da zakulo sabbin garuruwa a nahiyar Afrika, Asiya, Turai da sauran su, wadanda suke ganin mutum zai more kallo idan ya ziyarce su.
Kasar Jojiya ita ce ta kasance a sahun farko a jadawalin, kasancewarta ƙasa mai cike da al'adu, gine-ginen tarihi da wuraren yawan bude ido.
Asali: Legit.ng