Manyan kasashen duniya guda goma da suka fi farin ciki da jin dadin rayuwa

Manyan kasashen duniya guda goma da suka fi farin ciki da jin dadin rayuwa

A yayin da duniya ta rike ta kuma dimauce akan cuta mai kisa da ta addabi kowacce kasa ta duniya wato Coronavirus, zai zama kamar ba yanzu ne ya kamata a bayyana kasashen da suka fi farin ciki a duniya ba

Amma dai duniya ta fitar da rahoton kasashen da suka fi farin ciki a duniya a shekarar 2019, inda ta bayyana kasar Finland a matsayin ta farko a bangaren farin ciki da jin dadin rayuwa.

Haka kuma rahoton yana duba kasashe akan abubuwa guda shida da suka hada da tattalin arziki, jin dadin rayuwa, harkar lafiya, walwala, kirki da mutunci tsakanin al'umma, rashin cin hanci da rashawa.

A yadda rahoton ya bayar kasar da tafi kowacce ita ce kasar Finland, wacce take a yankin Turai. Sannan sauran kasashe biyar na cikin jerin duka daga yankin Turai ne.

KU KARANTA: Babbar magana: Daya daga cikin makusantan mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya kamu da cutar Coronavirus

Daga kasar Finland sai kasar Denmark, Norway, Iceland da kuma kasar Netherlands.

Najeriya da take da yawan mutane sama da miliyan 200 ta zama kasa ta 85 a duniya.

Kasar Sudan ta Kudu ita ce kasar da ta zo ta karshe a duniya, kasar ta zama mutanen cikinta basa jimawa a duniya, bata da karfin tattalin arziki.

Kamar yadda rahoton ya bayar na shekarar 2019, ga jerin kasashen guda goma a kasa:

1. Finland

2. Denmark

3. Norway

4. Iceland

5. Netherlands

6. Switzerland

7. Sweden

8. New Zealand

9. Canada

10. Austria

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel