Gwamnan PDP Ya Fusata Kan Kisan Babban Jigo a APC, Ya Ba Jami'an Tsro Muhimmin Umarni

Gwamnan PDP Ya Fusata Kan Kisan Babban Jigo a APC, Ya Ba Jami'an Tsro Muhimmin Umarni

  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya nuna alhihininsa kan kisan da aka yiɓwa sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar APC a jihar
  • Gwamnan ya bayyana kisan a matsayin babban zalunci da rashin sanin daraja da ƙimar da ran ɗan Adam yake da ita
  • Ya umarci jami'an tsaro da su gaggauta farauto miyagun da suka aikata wannann ɗanyen aikin domin su fuskanci hukunci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang, ya umurci hukumomin tsaro da su yi gagawar ganowa tare da gurfanar da waɗanda suka kashe sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na jihar, Hon. Sylvanus Namang.

Wasu miyagu ne dai suka halaka sakataren yaɗa labaran a ranar Asabar, 17 ga watan Fabrairun 2024, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Zanga-zanga ta barke a fadar babban basarake a Arewa? Gaskiya ta bayyana

Gwamna Mutfwang ya yi ta'aziyya a Plateau
Gwamna Mutfwang ya umarci jami'an tsaro su gano makasan Sylvanus Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Gwamnan, a wani saƙon ta’aziyya da ya aike a ranar Talata, ya bayyana matuƙar bakin ciki da ɓacin ransa game da kisan gillar da aka yi a Pankshin a daren ranar Asabar, yana mai cewa dole ne a kama waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin fuskantar fushin doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamnan ya ce kan kisan?

Gwamnan ya bayyana kisan a matsayin aikin ta'addanci wanda ya keta haddin daraja da ƙimar da ran ɗan Adam yake da ita, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Mutfwang ya jajanta wa al'ummar Mwaghavul, jam'iyyar APC, jihar Plateau da duk waɗanda suka sani kuma suka yi aiki tare da marigayi Namang.

Ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ba kawai ga iyalansa da jam'iyyar APC kaɗai ba, har ma da jihar da ƙasa baki ɗaya.

Hakazalika, gwamnan ya jajanta wa iyalan marigayi Mista Sunny Okonkwo, wanda shi ma wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kashe shi, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan mutane da dama sun rasu a wani mummunan hatsarin mota

Gwamna Mutfwang Ya Kori Shugabannin Manyan Makarantu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya koti shugabannin manyan makarantun gaba da sakandare guda biyar a jihar.

Shugabannin sun haɗa da na kwalejin fasaha ta jihar Plateau, Barkin Ladi, kwalejin fasaha ta lafiya, Pankshin, kwalejin fasaha ta lafiya, Zawan da kwalejin ilmi da ke Gindiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng