Allah ya yiwa mai kula da masallacin Manzon Allah, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa

Allah ya yiwa mai kula da masallacin Manzon Allah, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa

  • Daya daga cikin wadanda suka fi dadewa suna yi wa Masallacin Manzon Allah S.A.W hidima Agha Habeeb Muhammad al-Afari, ya kwanta dama
  • Muhammad al-Afari, wanda ke kula da dakin da kabarin Mazon Allah S.A.W yake ya rasu a yau Laraba, 13 ga watan Yuli
  • Za a yi jana'izar Marigayi Muhammad al-Afari a Masallacin Manzon Allah a yau bayan sallar Magaruba

Allah ya yiwa daya daga cikin wadanda suka dade suna yi wa Masallacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi hidima, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa.

Marigayin shine kuma ke kula da dakin da kabarin Annabi Muhammad yake.

Massalacin Annabi
Allah ya yiwa mai kula da masallacin Manzon Allah, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa Hoto: @hsharifain
Asali: Twitter

Muhammad al-Afari ya rasu ne a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, kamar yadda shafin Haramain Sharifain @hsharifain ya wallafa a Twitter.

Za a yi Sallah janaizarsa a masallacin Annabi a yau Laraba bayan sallar Magariba.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyo: Dandazon jama'a sun fito nuna wa Buhari kauna yayin da yake takawa zuwa gida daga idi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jami'an tsaro a kasar Saudi Arabia sun damke mabarata a Masjid Al-Haram

A wani labari na daban, jami'ai a kasar Saudi sun yi ram da mazauna da masu karya dokar da aka kama suna bara a Makkah, wadanda suka hada da cikin dukkan manyan masallatai 2 na Annabi, jaridar The Islamic Inforrmation ta ruwaito.

Kamar yadda hukumomin Saudi suka bayyana, an yi ram da wani mazaunin kasar 'dan kasar Indiya a harabar babban masallacin da wani 'dan kasar Morocco a wajen masallacin bayan an kamasu suna bara don su samu tausayawa daga masu bauta.

Haka zalika, Saudi Gazette ta ruwaito cewa, an hada da wani da ya karya doka 'dan kasar Yemen a jerin sunayen wadanda aka kama, wanda ya yi amfani da sandar guragu ya nuna cewa yana da nakasa don ya roki mutane.

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotunan Buhari da Yusuf a Filin Sallar Idin Babbar Sallah Sun Kayatar

Asali: Legit.ng

Online view pixel