Indiya Ta Rushe Masallacin Juma’a Mai Shekaru 600 a New Delhi, an Lalata Kaburbura a Wurin Ibadar

Indiya Ta Rushe Masallacin Juma’a Mai Shekaru 600 a New Delhi, an Lalata Kaburbura a Wurin Ibadar

  • Gwamnatin Indiya ta rushe Babban masallacin Juma’a da ke da tarihi mai shekaru fiye da 600 a birnin New Delhi
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gangamin cewa a rushe masallatan don maye gurbinsu da wuraren bautar Hindu
  • Mamban kwamitin masallacin ya ce ko kwafin Alkur’ani daya ba su dauka ba inda ya ce babu sanarwa aka fara rushe masallacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

New Delhi, Indiya – Gwamnatin Indiya ta rushe masallacin Juma’a mai cike da tarihi a birnin New Delhi da ke kasar.

Masallacin akalla ya kai shekaru 600 a duniya wanda ya ke dauke da tarihi na musamman a kasar, cewar TRT World.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya rufe wurin ibada kan damun jama'a da kara, ya gargadi mutane kan saba dokar

Indiya ta rushe babban masallaci mai tarihi a New Delhi
An Kange Harabar Masallacin da Indiya Ta Rushe Mai Shekaru 600 a New Delhi. Hoto: AFP.
Asali: AFP

Yaushe aka rushe masallacin a Indiya?

Wannan rushe masallacin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gangamin cewa a rushe masallatan don maye gurbinsu da wuraren bautar Hindu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masallacin Akhonji da ke birnin New Delhi ya kai shekaru 600 sannan ya na dauke da dalibai da ke makarantar kwana a cikinsa.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata 30 ga watan Janairu kusa da dajin Mehrauli da ke wajen birnin, cewar Times of India.

Martanin kwamitin masallacin

Mohammed Zaffar wanda mamban kwamitin masallacin ne ya ce ba su samu wata sanarwa ba kafin rushe masallacin.

Zaffar ya ce akwai kaburbura da dama a cikin masallacin wanda aka lalata su kuma babu wanda aka bari ya dauki ko da kwafin Alkur’ani daya ne da sauran kayayyaki.

Ya ce:

"Mafi yawan magabatanmu da kakanninmu duk an binne su a nan, babu wani alamun kaburburan yanzu.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya bayyana mugun mawuyacin hali da za a shiga idan ba a cire tallafi ba

"Buraguzan masallacin da kaburburan duka an kwashe zuwa wani wuri na daban kuma nesa da wurin."

Indiya ta kulle makarantar da aka ci zarafin Musulmi

Kun ji cewa Hukumomi a kasar Indiya sun ba da umarnini rufe makaranta a Arewacin jihar Uttar Pradesh bayan cin zarafin dalibi Musulmi.

Ana zargin wata malamar makarantar da ba da umarnin yi wa wani dalibi Musulmi taron dangin maruka.

A cikin wani faifan bidiyo, an gano wani dalibi mai shekaru bakwai na tsaye inda malamar ta ke umurtan daliban daya bayan daya su ta so suna marinshi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.