An Ci Tarar Wani Kamfanin Amurka Dala 70,000 Saboda Ya Tilasta Ma’aikaci Musulmi Ya Aske Gemu
- Wani kamfanin Amurka mai suna Blackwell zai biya tarar dala dubu 70 bayan da ya tilasta wani ma'aikaci Musulmi aske gemunsa
- Hukumar tabbatar da daidaito a wajen daukar aiki ta Amurka EEOC ce ta shigar da karar bayan gaza cimma sasanci da kamfanin
- An ruwaito cewa, kamfanin ya ba ma'aikacin zabi kan aske gemunsa ko rasa aikinsa, wanda hakan ya sa ma'aikacin zabar aske gemun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Kotu ta ci tarar wani kamfanin Amurka, Blackwell Security Services Inc., dala dubu 70 saboda ya nemi wani ma'aikaci Musulmi ya aske gemu.
Hukumar tabbatar da daidaito wajen daukar aiki ta Amurka (EEOC) ta shigar da karar kamfanin bisa tuhumar karya dokar daukar aiki da hakkin ma'aikata.
Hukumar EEOC ta zargi kamfanin da kin karbar tsarin addinin ma'aikacin, tare da tilasta shi zabar aikinsa ko addininsa, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin ya nemi ma'aikacin ya zabi addini ko aikinsa
A cewar EEOC, ma'aikacin na da ikon tafiyar da rayuwarsa bisa tafarkin addinin da ya ke ciki ba tare da wata wariya ba.
An ruwaito cewa kamfanin Blackwell ya nemi mutumin ya sake gemunsa ma damar yana son yin aiki a kamfanin.
Lokacin da ya nemi a bashi damar barin gemunsa saboda addini, sau kamfanin ya ce zai sallame shi ma damar ba zai aske ba.
Kotu ta ci tarar kamfani saboda karya dokar sashe na VII
Hukumar ta ce ma'aikacin ya aske gemun nasa ba da son ransa ba, sai don gudun kar ya rasa aikin.
Ta ce wannan laifi ya saba da sashe na VII na dokar 'yancin dan Adam ta 1964, wacce ta haramta nuna bambanci kan addini tsakani ma'aikaci da inda yake aiki.
Bayan gaza cimma wata yarjejeniya da kamfanin ne ya sa hukumar ta shigar da kara kotun lardi ta Arewacin Illinois.
Jerin kasashen duniya 5 da ya kamata ku ziyarta
A wani labari kuma, Legit Hausa ta tattaro bayani kan wasu kasashen duniya 5 da ya kamata ku ziyarta a wannan shekarar ta 2024 don yawon bude ido.
Kasashen wadanda suka hada da Oman da Madagaska, sun kasance cike da gine-gine, al'adu, da abubuwan ban mamaki wadanda za su nishadantar da mutae.
Asali: Legit.ng