Kungiyar kare yancin dan adam ta soki CP Wakili bisa kama mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar kare yancin dan adam ta soki CP Wakili bisa kama mataimakin gwamnan Kano

-Kama Nasiru Gawuna na cike da son kai, inji kungiyar kare yancin dan adam

-Yakamata ace hukumar yan sanda na aikine ba tare da nuna son kai ba kana kuma a bisa bin dokokin kasa, a cewar kungiyar kare yancin dan adam

Kungiyar kare yancin dan adam tace Kwamishinan yan sandan Kano Mohammed Wakili sam bai kyauta ba saboda kama mataimakin gwamnan Nasiru Gawuna da yan sanda sukayi yayinda da akayi zaben gwamnan jihar a cikin watan Maris.

Kungiyar kare yancin dan adam ta soki CP Wakili bisa kama mataimakin gwamnan Kano
CP Muhammad Wakili
Asali: Twitter

KU KARANTA:APC: Sabon karancin albashin N30,000 dayane daga cikin alkawuranmu da muka cika

Zancen da ya fito daga kungiyar wanda Ramat A. Ibrahim ta sanya ma hannu gami da majalisar dinkin duniya da kuma Amnesty international na cewa, kama mataimakin gwamnan yaci karo da doka.

“Kwamishina Wakili, yayi ainihin nuna son kaine akan senata Rabi’u Kwankwaso yayinda kawai ya kama mataimakin gwamna ba tare da ya kama Rabi’u Musa Kwankwaso ba duk da tayar da zaune tsaye da yayi a lokacin zaben ta hanyar amfani da matasa. Wannan batun sun fadeshi ne a kafafen rediyo cikin wani shiri na musamman.

“Zancen ya kara da cewa idan kwamishinan zai iya sabawa doka ta hanyar kama mataimakin gwamnan duk da kariyar dake gareshi, a daidai lokacinda ga wasu matasa na fitinar al’umma da rikice-rikice su kuma an gagara kamasu. Wannan shi zai tabbar maka da cewa akwai son kai a cikin wannan abu.” 

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng