Taliban ta haramta wa wanzamai aske wa mutane gemu, ta hana sauraron waƙoƙi a Afghanistan

Taliban ta haramta wa wanzamai aske wa mutane gemu, ta hana sauraron waƙoƙi a Afghanistan

  • Sabuwar gwamnatin Taliban a Afghanistan ta yi sabon doka na haramtawa wanzamai aske gemun mutane
  • Har ila yau sabuwar gwamnatin na musulunci ta kuma haramta saka wakoki da sauraronsu a wuraren wanka da sauran wurare a gari
  • Gwamnatin ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana saba dokokin zai fuskanci hukunci bisa shari'a kuma ba shi da ikon yin korafi

Afghanistan - An haramta wa wanzamai a yankin Helmand aske wa mutane gemunsu da saka wakoki a rediyo ko talabijin a shagunan aski, Daily Trust ta ruwaito.

Taliban ta haramta wa wanzamai aske wa mutane gemu, ta hana sauraron waƙoƙi a Afghanistan
Wanzami yana yi wa wani mutum aski. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, sashin habbaka tarbiya da kare aikata masha'a na yankin ya umurci wanzamai da masu askin zamani su yi biyayya ga sabon umurnin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da malami a Kaduna

Sanarwar ta ce:

"Daga yau, an hana aske gemun mutane da sauraron wakoki a shagon aski da gidajen wanka na gari."
"Idan aka samu wani wanzami ya aske gemun wani ko gidan wanka na gari yana saka wakoki, za a hukunta su bisa tanadin shari'a kuma ba su da ikon su shigar da wani korafi."

Wannan sabon dokar yana daga cikin sabbin dokoki da ka'idoji da sabuwan gwamnatin Taliban ta farfado da su ne karkashin gwamnatin ta na musulunci.

Tun bayan Taliban sun amshi mulkin Afghanistan a ranar 15 ga watan Augusta su ka yi alkawarin ci gaba da hukuncin da suka saba a baya amma da dan sassauci.

Taliban: Gwamnatin mu za ta dawo da datse hannun ɓarayi da sauran hukunce-hukuncen shari'ar musulunci

A wani labarin mai kama da wannan, tsohon shugaban ‘yan sandan Taliban yace za su ci gaba da hukunce-hukunce kamar yanke gabobin masu laifi a Afghanistan.

Kara karanta wannan

Daga bisani, NYSC ta ce ita ta fitar da shawarar biyan kudin fansa, za ta fara bincike a kai

Kamar yadda Arise Tv ta ruwaito, Mullah Nooruddin Tarabi wanda shine mai kula da gidajen yarin kasar Afghanistan ya sanar da AP News cewa wajibi ne su ci gaba da hukunce-hukuncen saboda tsaro.

A cewar sa ba lallai a dinga hukuncin a gaban mutane ba kamar yadda suke yi a baya.

A cewar sa:

“Babu wanda ya isa ya fada mana abinda ya dace mu yi.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164