Ana Tare Har Gobe: Kungiyar ECOWAS Ta Maida Martani ga Ficewar Nijar da Kasashe 2

Ana Tare Har Gobe: Kungiyar ECOWAS Ta Maida Martani ga Ficewar Nijar da Kasashe 2

  • ECOWAS ba ta san da zancen ficewar wasu kasashe daga cikinta ba, akasin labarin da yake yawo a Afrika
  • A wata sanarwa ta musamman, kungiyar kasashen yammacin Afrika tace ba ta samu labari a hukumance ba
  • Kungiyar ECOWAS tace tana da burin kawo karshen gwamnatin sojoji a Mali, Nijar da kuma Burkina Faso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - ECOWAS ta kasashen yammacin nahiyar Afrika tayi watsi da sanarwa da aka bada na ficewar wasu daga cikin ‘ya ‘yanta.

Kungiyar ta ECOWAS ta musanya cewa kasar Jamhuriyyar Nijar, Mali da Burkina Faso sun balle daga tafiyar da ake yi tun 1975.

ECOWAS
Shugabannin ECOWAS Hoto: @ecowas_cedeao, businesslive.co.za
Asali: Twitter

Shugabannin ECOWAS sun yi martani

A sanarwar da ta fito daga shafin ECOWAS a dandalin X, an fahimci har yanzu kungiyar na neman kawo karshen mulkin soji.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari sun jawo za a binciki inda Gwamnoni 150 da Ministoci Suka Kai N40tr

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Lahadi, ECOWAS tace tana kokari wajen ganin an dawo da mulkin farar hula a kasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso.

Sanarwar tace har yanzu kasashen nan da ake magana suna cikin ECOWAS, kuma suna cikin ‘ya ‘yan da ake ba muhimmanci.

Daily Trust tace ana so a shawo kan sabanin siyasar da ke tsakanin shugabanni da gwamnatocin kasashen nan da kungiyar nan.

Jawabin kungiyar ECOWAS

"Hankalin hukumar kasashen Afrika ta yamma ya je ga wani jawabi da aka fitar a gidajen talabijin kasashen Mali da Nijar"
"Inda aka sanar da matakin Burkina Faso, Mali da Nijar daga ficewa daga ECOWAS."
"Har yanzu kungiyar ECOWAS ba ta samu sanarwa a hukumance daga kasashen nan uku game da niyyarsu na janye jiki ba."

- ECOWAS

Premium Times tace shugabannin ECOWAS za su sa sanar da al’ummar kasashen halin da ake ciki domin jin matakin da za a dauka.

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Legas ya shaki iskar 'yanci

Meya jawo sabani a ECOWAS?

Shehu Shehu yana zargin cewa biyewa kasashen yamma da wasu suka yi ne ya yi sanadiyyar rabuwar kai a tafiyar ta ECOWAS.

'Dan siyasa kuma 'dan gwagwarmayar na Najeriya ya koka game da yadda aka gaza amfani da hanyar lalama wajen dinke baraka.

ECOWAS ta maka takunkumi

Kwanaki aka samu labari Muhammadu Sanusi II ya roki shugabannin ECOWAS su gaggauta janye takunkumin da ke kan kasar Nijar.

Sanusi II ya yi tir da yadda aka yi watanni babu lantarki, abinci da maganguna a makwabtan Najeriyan saboda an yi juyin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng